Musulunci > Ha > Hadith > Falaloli da ladubba > Wanda ya shiryar a kan wani alheri, to, shi ma yana da kwatankwacin ladan wanda ya aikatas…
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1عن أبي مسعود الأنصاري رضي الله عنه قال: جَاءَ رَجُلٌ إِلَى النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَقَالَ: إِنِّي أُبْدِعَ بِي فَاحْمِلْنِي، فَقَالَ: «مَا عِنْدِي»، فَقَالَ رَجُلٌ: يَا رَسُولَ اللهِ، أَنَا أَدُلُّهُ عَلَى مَنْ يَحْمِلُهُ، فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَنْ دَلَّ عَلَى خَيْرٍ فَلَهُ مِثْلُ أَجْرِ فَاعِلِهِ».
Wani mutum ya zo ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai ya ce: Lallai cewa dabbata ta halaka, ka ɗorani a kan wata dabbar, kuma ka ba ni wani abin hawan da zai kai ni, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ba shi uzuri cewa ba shi da wani abin da zai dorashi a kansa, sai wani mutum da ya ke wurin ya ce: Ya Manzon Allah, ni zan shiryar da shi ga wanda zai ba shi dabbar da za ta ɗaukeshi, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ba da labarin cewa ya zama abokin tarayyar mai sadakar a lada; domin ya shiryar da mabuƙacin zuwa gareshi.
Rukunan : FIƘHUN HALAYE · HALAYE NAGARI · FALALOLI DA LADUBBA