Lallai Allah Ya yi mini wahayi cewa ku ƙanƙar da kai, har kada wani ya yi wa wani alfahar…
Musulunci > Ha > Hadith > Fihun halaye > Lallai Allah Ya yi mini wahayi cewa ku ƙanƙar da kai, har kada wani ya yi wa wani alfahar…
Wanda ya ruwaito hadisin: Muslim ne ya rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Lallai Allah Ya yi mini wahayi cewa ku ƙanƙar da kai,…
Bayanin hadisin: Lallai Allah Ya yi mini wahayi cewa ku ƙanƙar da kai,…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya miƙe a cikin sahabbansa yana mai huɗuba, ya kasance daga cikin abinda ya ce: Lallai cewa Allah Ya yi masa wahayi cewa ya wajaba akan mutane su yi tawali'u a tsakaninsu, hakan ta hanyar ƙanƙar da kai ga halitta da tausasa lamura, har kada wani ya yi alfahari ta hanyar da'awar girma da kafafa da ɗaukakar da zai danganta kansa ko dukiyarsa ko wanin haka akan wani, kuma kada wani ya zalinci wani, kuma kada ya yi ta'addaci akan wani.
Koyarwar hadisin: Lallai Allah Ya yi mini wahayi cewa ku ƙanƙar da kai,…
- A cikin hadisin akwai kwaɗaitarwa akan tawali'u da rashin girman kai da rena mutane.
- Hani daga zalinci da kuma alfahari.
- Yi wa Allah tawali'u yana da ma'anoni biyu: Ma'ana ta farko: Ita ce, ka yi wa Addinin Allah tawali'u, kada ka rena Addini, kuma kada ka yi masa girman kai akan sauke hukunce-hukuncensa. Na biyu: Ka yi wa bayin Allah tawali'u saboda Allah, badan tsoronsu ba, ba kuma dan kwaɗayin abinda ke gurinsu ba, sai dai saboda Allah - Mai girma da ɗaukaka -.
Rukunan :
FIƘHUN HALAYE
· ABUBUWA MASU TAUSASA ZUKATA DA WA'AZOZI
· HALAYE NAGARI
· AYYUKAN ZUKATA
· FALALOLI DA LADUBBA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
حسبنا الله ونعم الوكيل
Allah Ya isa mana, Shi ne mafi kyawun Mai Kiyaye