Haƙƙin musulmi akan musulmi guda shida ne" aka ce: Waɗannene su ya Manzon Allah?, ya ce: "…
Musulunci > Ha > Hadith > Hukunce hukuncen auna da barranta > Haƙƙin musulmi akan musulmi guda shida ne" aka ce: Waɗannene su ya Manzon Allah?, ya ce: "…
Wanda ya ruwaito hadisin: Muslim ne ya rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Haƙƙin musulmi akan musulmi guda shida ne" aka ce: Waɗa…
Bayanin hadisin: Haƙƙin musulmi akan musulmi guda shida ne" aka ce: Waɗa…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa daga haƙƙin musulmi akan ɗan uwansa musulmi ɗabi'u shida ne: Na farko: Idan ya haɗu da shi ya yi masa sallama da faɗin: Assalamu alaikum, Wato: Aminci ya tabbata agare ku, shi kuma ya dawo da sallama da faɗinsa: Waalaikumus Salam, Wato: Aminci ya tabbata agare ku. Na biyu: Amsa gayyatarsa idan ya gayyace shi dan walima da makamancinta. Na uku: Yi masa nasiha idan ya nemeta, kada ka yi masa yaudara ko ka yi masa algus. Na huɗu: Idan ya yi atishawa sai ya ce: Godiya ta tabbata ga Allah, to ka gaishe shi da faɗin: (Yarhamukallah) Allah Ya yi maka rahama, shi kuma ya amsa yana mai cewa: Allah Ya shiryar da ku kuma ya gyara zuciyarku. Na biyar: Ya gaishe shi kuma ya ziyarceshi idan ya yi rashin lafiya. Na shida: Ya yi masa sallah idan ya rasu, kuma ya bi jana'izarsa har sai an binne shi.
Koyarwar hadisin: Haƙƙin musulmi akan musulmi guda shida ne" aka ce: Waɗa…
- Shaukani ya ce: Abin nufi da faɗinsa: (Haƙƙin musulmi) cewa barinsa bai kamata ba, kuma aikatashi yana zama kodai wajibi ko mandubi mai ƙarfi mai kama da wajibin da barinsa ba ya kamata.
- Maida sallama farilla ce ta aini idan wanda aka yi wa sallamar shi kaɗai ne, kuma mutum ɗaya ya isarwa jama'a, amma fara sallama to asali a cikinsa shi ne sunnah.
- Ziyarar mara lafiya yana daga haƙƙoƙinsa akan 'yan uwansa musulmai; domin cewa ziyara tana shigar da farin ciki da kewa a zuciyarsa, kuma ita farilla ce ta kifaya.
- Wajabcin amsa gayyata muddin dai babu wani zunubi a cikinta; idan ta kasance zuwa walimar angwanci ce to jumhur sun tafi akan wajabcin amsata sai dai inda wani uzuri na shari'a, amma idan ta kasance ba walimar angwanci ba ce to jumhur sun tafi a kan cewa sunnah ce.
- Gaishe da mai atishawa wajibi ne akan wanda ya ji godiyar (Allah) ga wanda ya yi atishawa ɗin.
- Cikar shari'a da kwaɗayinta a cikin ƙarfafa igiyar zamantakewa da imani da alaƙar soyayya tsakanin ɗaiɗaiku.
- (Fasammithu) a cikin wasu bugun: (Fashammithu), da Sin mara 'ya'ya da kuma Shin mai 'ya'ya: Addu'a da alheri da kuma albarka, al-Tashmit an ce a cikin ma'anarta: Allah Ya nisantar da kai daga dariyar ƙeta, kuma Ya nisantar da kai abinda maƙiyinka zai yi maka dariyar ƙeta da shi, Tasmit kuma ma'anarsa: Allah Ya shiryar da kai zuwa hanya madaidaiciya.
Rukunan :
HUKUNCE-HUKUNCEN ƘAUNA DA BARRANTA
· LADUBBA NA SHARI'A
· LADUBBAN ATISHAWA DA NA HAMMA
· ILIMIN AƘIDA
· FALALOLI DA LADUBBA
· ƘAUNA DA BARRANTA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
حسبنا الله ونعم الوكيل
Allah Ya isa mana, Shi ne mafi kyawun Mai Kiyaye