Lallai mutane idan suka ga azzalumi ba su yi riƙo da hannayensa ba, ya kusa Allah Ya games…

Musulunci > Ha > Hadith > Umarni da kyakkyawa da hani daga mummuna > Lallai mutane idan suka ga azzalumi ba su yi riƙo da hannayensa ba, ya kusa Allah Ya games…

Wanda ya ruwaito hadisin: Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i cikin alkubra da Ibnu Majah haka kuma Ahmad

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 1

Rubutun hadisin: Lallai mutane idan suka ga azzalumi ba su yi riƙo da ha…

Bayanin hadisin: Lallai mutane idan suka ga azzalumi ba su yi riƙo da ha…

(Sayyidina) Abubakar Siddiƙ - Allah Ya yarda da shi - yana bada labari: Cewa mutane suna karanta wannan ayar:

{Yaku waɗanda suka yi imani ku lizimci kawunanku, wanda ya ɓata ba zai cutar daku ba idan kun shiriya} [al-Ma'ida: 105].

Suna fahimta daga ayar cewa ya wajaba ga mutum ya yi ƙoƙari ya gyara kansa kawai, kuma ɓatan wanda ya ɓata ba zai cutar da shi ba bayan hakan, kuma su ba’a nema daga gare su su yi umarni da kyakkyawa kuma su hana mummuna ba.

Sai ya sanar da su cewa ita ayar ba haka take ba, cewa shi ya ji annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: Lallai mutane idan suka ga azzalimi ba su hana shi zalincin ba, kuma suna da iko akan hana shin, ya kusa Allah Ya game su baki ɗaya da uƙuba daga gareShi, mai aikata abin ƙin, da mai yin shiru bai hana ba.

Koyarwar hadisin: Lallai mutane idan suka ga azzalumi ba su yi riƙo da ha…

Rukunan : UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DAGA MUMMUNA · HUKUNCIN UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DAGA MUMMUNA · DA'AWA DA HISBA

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
حسبنا الله ونعم الوكيل Allah Ya isa mana, Shi ne mafi kyawun Mai Kiyaye

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah