Wanda ya rantse da wanin Allah to hakika ya kafirta ko ya yi shirka

Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > Wanda ya rantse da wanin Allah to hakika ya kafirta ko ya yi shirka

Wanda ya ruwaito hadisin: Abu Daud ne ya ruwaito shi da Kuma Tirmizi da Ahmad

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 1

Rubutun hadisin: Wanda ya rantse da wanin Allah to hakika ya kafirta ko…

عن ابْنِ عُمَرَ رضي الله عنهما أنه سَمِعَ رَجُلًا يَقُولُ: لَا وَالْكَعْبَةِ، فَقَالَ ابْنُ عُمَرَ: لَا يُحْلَفُ بِغَيْرِ اللَّهِ، فَإِنِّي سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «مَنْ حَلَفَ بِغَيْرِ اللهِ فَقَدْ كَفَرَ أَوْ أَشْرَكَ».

Bayanin hadisin: Wanda ya rantse da wanin Allah to hakika ya kafirta ko…

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bada labarin cewa wanda ya yi rantsuwa da wanin Allah da sunayensa da siffofinsa to hakika ya kafircewa Allah ko ya yi shirka; domin rantsuwa tana hukunta girmama wanda aka rantse da shi, girma kadai ya tabbata ga Allah ne Shi kadai; ba'a rantsuwa sai da Allah da sunayensa da siffofinsa - tsarki ya tabbatar masa, Wannan rantsuwar tana daga karamar shirka; saidai da a ce mai rantsuwa ya girmama abinda ya rantse da shi kamar girmama Allah - Madaukakin sarki - ko sama da haka; to a wannan lokacin zai zama daga babbar shirka.

Koyarwar hadisin: Wanda ya rantse da wanin Allah to hakika ya kafirta ko…

Rukunan : ILIMIN AƘIDA · SUNAYE DA HUKUNCE-HUKUNCE · SHIRKA

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 97%
Wata Sabo a cikin kwana 13
أستغفر الله Ina neman gafara daga Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah