Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > ya rabauta idan gasgata hakan
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 2عَنْ طَلْحَةَ بْنِ عُبَيْدِ اللهِ رضي الله عنه قَالَ: جَاءَ رَجُلٌ إِلَى رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ مِنْ أَهْلِ نَجْدٍ ثَائِرُ الرَّأْسِ، نَسْمَعُ دَوِيَّ صَوْتِهِ، وَلَا نَفْقَهُ مَا يَقُولُ حَتَّى دَنَا مِنْ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَإِذَا هُوَ يَسْأَلُ عَنِ الْإِسْلَامِ، فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «خَمْسُ صَلَوَاتٍ فِي الْيَوْمِ وَاللَّيْلَةِ» فَقَالَ: هَلْ عَلَيَّ غَيْرُهُنَّ؟ قَالَ: «لَا، إِلَّا أَنْ تَطَّوَّعَ، وَصِيَامُ شَهْرِ رَمَضَانَ»، فَقَالَ: هَلْ عَلَيَّ غَيْرُهُ؟ فَقَالَ: «لَا، إِلَّا أَنْ تَطَّوَّعَ»، وَذَكَرَ لَهُ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ الزَّكَاةَ، فَقَالَ: هَلْ عَلَيَّ غَيْرُهَا؟ قَالَ: «لَا، إِلَّا أَنْ تَطَّوَّعَ»، قَالَ: فَأَدْبَرَ الرَّجُلُ، وَهُوَ يَقُولُ: وَاللهِ، لَا أَزِيدُ عَلَى هَذَا، وَلَا أَنْقُصُ مِنْهُ، فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «أَفْلَحَ إِنْ صَدَقَ».
Wani mutum daga cikin mutanen Najad ya zo wurin annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - gashinsa ya yi datti, kuma muryarsa mai ƙarfi, ba'a fahimtar abinda yake faɗa, har ya kusanto ga annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya yi tambaya game da farillan musulunci?
Sai annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fara da sallah, kuma ya sanar da shi cewa Allah Ya faralanta masa salloli biyar a cikin kowanne yini da dare.
Sai ya ce: Shin wani abu daga salloli sun wajaba a kaina banda waɗannan biyar ɗin?
Sai ya ce: A'a, sai dai idan ka yi nafila daga sallolin nafila.
Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Daga abinda Allah Ya wajabta shi akanka azumin watan Ramadan.
Sai mutumin ya ce: Shin akwai wani abu na azimi da ya wajaba a kaina banda azimin Ramadan?
Sai ya ce: A'a, saidai idan ka yi nafila da wani azimi.
Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ambata masa zakka.
Sai mutumin ya ce: Shin wani abu na sadaka bayan farillar zakka ya wajaba a kaina?
Ya ce: A'a, saidai idan ka yi nafila.
Bayan mutumin ya ji waɗannan bayanai daga manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya juya baya ya yi rantsuwa da Allah - Maɗaukakin sarki - cewa shi zai dawwama a kansu ba tare da ƙari ko ragi ba, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce bayan haka: Idan ya gasgata abinda ya faɗa akan abinda ya rantse akansa to shi zai zama daga masu rabauta.
Rukunan : ILIMIN AƘIDA · SUNAYE DA HUKUNCE-HUKUNCE · MUSULUNCI