Ya kai yaro, zan sanar da kai wasu kalmomi, ka kiyaye Allah Zai kiyayeka, ka kiyaye Allah …

Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > Ya kai yaro, zan sanar da kai wasu kalmomi, ka kiyaye Allah Zai kiyayeka, ka kiyaye Allah …

Wanda ya ruwaito hadisin: Tirmizi ne ya ruwaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Ya kai yaro, zan sanar da kai wasu kalmomi, ka kiyaye A…

عن ابن عباس رضي الله عنهما قال: كُنْتُ خَلْفَ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَوْمًا، فَقَالَ: «يَا غُلَامُ، إِنِّي أُعَلِّمُكَ كَلِمَاتٍ، احْفَظِ اللهَ يَحْفَظْكَ، احْفَظِ اللهَ تَجِدْهُ تُجَاهَكَ، إِذَا سَأَلْتَ فَاسْأَلِ اللهَ، وَإِذَا اسْتَعَنْتَ فَاسْتَعِنْ بِاللهِ، وَاعْلَمْ أَنَّ الْأُمَّةَ لَوِ اجْتَمَعَتْ عَلَى أَنْ يَنْفَعُوكَ بِشَيْءٍ، لَمْ يَنْفَعُوكَ إِلَّا بِشَيْءٍ قَدْ كَتَبَهُ اللهُ لَكَ، وَلَوِ اجْتَمَعُوا عَلَى أَنْ يَضُرُّوكَ بِشَيْءٍ، لَمْ يَضُرُّوكَ إِلَّا بِشَيْءٍ قَدْ كَتَبَهُ اللهُ عَلَيْكَ، رُفِعَتِ الْأَقْلَامُ وَجَفَّتِ الصُّحُفُ».

Bayanin hadisin: Ya kai yaro, zan sanar da kai wasu kalmomi, ka kiyaye A…

Ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - yana ba da labarin cewa ya kasance yana ƙarami yana haye tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, sai (Annabi) tsira da aminci su tabbata a gare shi ya ce: Zan sanar da kai wasu al'amura da wasu abubuwan da Allah zai amfanar da kai su:

Ka kiyaye Allah ta hanyar kiyaye umarninsa da nisantar hane-hanensa, ta inda Zai sameka a ayyukan biyayya da kusanci, ka da Ya sameka a ayyukan saɓo da zunubai, idan ka aikata haka sakamakonka zai kasance shi ne Allah Zai kiyayeka daga abubuwan ƙi na duniya da lahira, kuma Zai taimakeka a ayyukanka a duk inda ka fuskanta.

Idan ka yi nufin roƙon wani abu, to, kada ka roƙi kowa sai Allah, to, haƙiƙa Shi kaɗai ne wanda yake amsawa masu roƙo.

Idan ka yi nufin neman taimako, to, kada ka nemi taimakon kowa sai Allah.

Kuma ya zama kana da yaƙini cewa wani amfani ba zai sameka ba, ko da mutanen duniya gaba ɗaya sun taru akan amfanarka sai dai abin da Allah Ya rubuta maka, kuma wani abin cutarwa ba zai faru a kanka ba, ko da mutanen duniya gaba ɗaya za su taru a kan cutarka, sai dai abin da Allah Ya ƙaddara a kanka.

Kuma wannan al'amarin tabbas Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya rubuta maka ya kuma ƙaddara shi daidai da abin da hikimarsa da saninsa suka hukunta, babu canji ga abin da Allah Ya rubuta.

Koyarwar hadisin: Ya kai yaro, zan sanar da kai wasu kalmomi, ka kiyaye A…

Rukunan : ILIMIN AƘIDA · Imani da Hukuncin Allah da Ƙaddara · MATAKAN HUKUNCIN ALLAH DA NA ƘADDARA

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 97%
Wata Sabo a cikin kwana 13
الله أكبر Allah Shi ne Mafi Girma

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah