Ba ya cikimmu wanda ya yi camfi, ko aka yi masa camfi, ko ya yi bokanci ko aka yi masa bok…

Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > Ba ya cikimmu wanda ya yi camfi, ko aka yi masa camfi, ko ya yi bokanci ko aka yi masa bok…

Wanda ya ruwaito hadisin: Bazzar ne Ya Rawaito shi

Hasan ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Ba ya cikimmu wanda ya yi camfi, ko aka yi masa camfi,…

عن عمران بن حصين رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «‌لَيْسَ ‌مِنَّا ‌مَنْ ‌تَطَيَّرَ أَوْ تُطُيِّرَ لَهُ، أَوْ تَكَهَّنَ أَوْ تُكُهِّنَ لَهُ، أَوْ سَحَرَ أَوْ سُحِرَ لَهُ، وَمَنْ عَقَدَ عُقْدَةً، وَمَنْ أَتَى كَاهِنًا فَصَدَّقَهُ بِمَا يَقُولُ فَقَدْ كَفَرَ بِمَا أُنْزِلَ عَلَى مُحَمَّدٍ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ».

Bayanin hadisin: Ba ya cikimmu wanda ya yi camfi, ko aka yi masa camfi,…

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi alƙawarin narkon azaba ga wanda ya aikata wasu ayyuka cikin al’ummarsa, da ya ce: Ba ya daga cikimmu.

Na farko: Wanda ya yi camfi ko aka yi masa camfi, asalinsa: suna sakin tsuntsu ne lokacin fara wani abu, kamar tafiya ko fatauci ko wanin haka, idan ya yi dama sai ya ce akwai sa’a, sai ya yi abin da ya sa a gaba, idan kuma ya yi hagu sai ya ce babu sa’a sai ya ƙi yi, bai halatta ya yi haka da kansa ba, ko ya sa a yi masa, camfi da kowanne abu na ji ne ko na gani ya shiga ƙarƙashin haka, da tsuntsaye ko dabbobi aka yi, ko masu fama da nakasa, ko wasu lambobi ko ranaku, da sauransu.

Na biyu: Wanda ya yi bokanci ko aka yi masa bokanci’. Duk wanda ya ce ya san gaibu ta hanyar taurari, ko wanin haka, ko ya je wurin wanda ya ce ya san gaibu kamar boka da makamantansu, ya kuma gasgata shi a abin da ya faɗa na cewar ya san gaibu, to, haƙiƙa ya kafirta da abin da aka saukarwa Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

Na uku: Wanda ya yi asiri ko aka yi masa asiri’. Shi ne wanda yake yin a siri da kansa, ko ya sa a yi masa asiri, domin ya amfanar da wani da shi, ko don ya cutar da wani, ko ya ƙulla ƙulli da zare da asiri da surkulle da aka haramta da tofi a kai.

Koyarwar hadisin: Ba ya cikimmu wanda ya yi camfi, ko aka yi masa camfi,…

Rukunan : ILIMIN AƘIDA · SUNAYE DA HUKUNCE-HUKUNCE · ABUBUWAN DA SUKE WARWARE MUSULUNCI · MAS'ALOLIN JAHILIYYA

بسم الله الرحمن الرحيم Lar 16 Jumada al-Awwal
الأربعاء 16 جمادى الأولى
أحدب متناقص Cikakken Wata Raguwa Rana 16.7 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
اللهم صل على محمد Ya Allah, ka saukar da tsira a kan Muhammad

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah