Lallai cewa ɗayanku ana tara halittarsa a cikin mahaifiyarsa kwana arba’in yana maniyyi

Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > Lallai cewa ɗayanku ana tara halittarsa a cikin mahaifiyarsa kwana arba’in yana maniyyi

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Lallai cewa ɗayanku ana tara halittarsa a cikin mahaifi…

عَنْ أَبِي عَبْدِ الرَّحْمَنِ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ مَسْعُودٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: حَدَّثَنَا رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَهُوَ الصَّادِقُ المَصْدُوقُ: «إِنَّ أَحَدَكُمْ يُجْمَعُ خَلْقُهُ فِي بَطْنِ أُمِّهِ أَرْبَعِينَ يَوْمًا، ثُمَّ يَكُونُ عَلَقَةً مِثْلَ ذَلِكَ، ثُمَّ يَكُونُ مُضْغَةً مِثْلَ ذَلِكَ، ثُمَّ يُرْسَلُ إلَيْهِ المَلَكُ فَيَنْفُخُ فِيهِ الرُّوحَ، وَيُؤْمَرُ بِأَرْبَعِ كَلِمَاتٍ: بِكَتْبِ رِزْقِهِ، وَأَجَلِهِ، وَعَمَلِهِ، وَشَقِيٍّ أَوْ سَعِيدٍ؛ فَوَالَّذِي لَا إلَهَ غَيْرُهُ إنَّ أَحَدَكُمْ لَيَعْمَلُ بِعَمَلِ أَهْلِ الجَنَّةِ حَتَّى مَا يَكُونُ بَيْنَهُ وَبَيْنَهَا إلَّا ذِرَاعٌ فَيَسْبِقُ عَلَيْهِ الكِتَابُ فَيَعْمَلُ بِعَمَلِ أَهْلِ النَّارِ فَيَدْخُلُهَا، وَإِنَّ أَحَدَكُمْ لَيَعْمَلُ بِعَمَلِ أَهْلِ النَّارِ حَتَّى مَا يَكُونُ بَيْنَهُ وَبَيْنَهَا إلَّا ذِرَاعٌ، فَيَسْبِقُ عَلَيْهِ الكِتَابُ فَيَعْمَلُ بِعَمَلِ أَهْلِ الجَنَّةِ فَيَدْخُلُهَا».

Bayanin hadisin: Lallai cewa ɗayanku ana tara halittarsa a cikin mahaifi…

Dan Mas'ud ya ce:: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zantar damu alhali shi mai gaskiyane a zancensa, kuma abin gasgatawa yayin da Allah - Madaukakin sarki - Ya gasgata shi. Ya ce: Lallai cewa dayanku ana taro halittarsa, cewa mutum idan ya zo wa iyalansa to tarwatsettsen maniyyinsa ana taroshi a cikin mace kwana arba'in yana maniyyi. Sannan ya zama gudan jini ita ce gudan jini mai kauri sandararre, wannan a arba'in ta biyu ne, Sannan ya zama gudan tsoka ita ce yanki na nama gwargwadan abinda ake taunawa, wannan a arba'in ta uku ce, Sannan sai Allah Ya aiko masa da Mala'ika, sai ya busa rai a cikinsa bayan karewar arba'in ta uku, Sai a umarci Mala'ikan da ya rubuta kalmomi hudu su ne: Arzikinsa, shi ne gwargwadan abin da zai samu daga ni'imomi a rayuwarsa, Da ajalinsa, shi ne gwargwadan wanzuwarsa a duniya, Da aikinsa, menene shi? dan wutan ne ko dan Aljanna ne. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi rantsuwa cewa; mutum zai yi aiki da aikin 'yan Aljanna kuma aikinsa zai zama na gari, wato a abinda yake bayyana ga mutane, kuma ba zai gushe a haka ba har ya kasance tsakaninsa da ita bai zama ba sai zira'i daya, wato: Babu abinda zai wanzu tsakaninsa da tsakanin saduwa da ita aljannar sai kamar wanda zai zama tsakaninsa da tsakanin wani wuri na kasa zira'i daya ne, sai littafi ya rinjaya akansa da abinda aka kaddara akansa to a wannan lokacin zai yi aiki da aikin 'yan wuta sai a cika masa da shi sai ya shiga wutar; Domin cewa sharadin karbar aikinsa shi ne ya tabbata akansa ta yadda ba zai canjaba, wani dayan kuma daga mutane zai yi ayyukan 'yan wuta har sai ya kusanci shigarta, kuma gwargwadan zira'i ne na kasa zai kasance tsakakninsa da wutar, sai littafi ya rinjaya akansa da abinda aka kaddara akansa, sai ya yi aikin 'yan Aljanna kuma ya shiga Aljannar.

Koyarwar hadisin: Lallai cewa ɗayanku ana tara halittarsa a cikin mahaifi…

Rukunan : ILIMIN AƘIDA · IMANI DA MALA'IKU · Imani da Ranar Lahira · Imani da Hukuncin Allah da Ƙaddara

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 97%
Wata Sabo a cikin kwana 13
اللهم صل على محمد Ya Allah, ka saukar da tsira a kan Muhammad

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah