Wanda ya rantse da amana to baya daga cikinmu
Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > Wanda ya rantse da amana to baya daga cikinmu
Wanda ya ruwaito hadisin: Abu Dawud ne ya Rawaito shi da Kuma Ahmad
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Wanda ya rantse da amana to baya daga cikinmu
Bayanin hadisin: Wanda ya rantse da amana to baya daga cikinmu
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hani kuma ya gargaɗar daga rantsuwa da amana, kuma cewa wanda ya aikata hakan to ba shi daga cikinmu.
Koyarwar hadisin: Wanda ya rantse da amana to baya daga cikinmu
- Haramcin rantsuwa da wanin Allah - Maɗaukakin sarki -, kuma daga cikin hakan: amana, kuma hakan yana daga ƙaramar shirka.
- Amana ta ƙunshi ɗa'a da bauta da ajiya da bayarwa hannu da hannu da amintarwa.
- Rantsuwa bata ƙulluwa sai da Allah - Maɗaukakin sarki - ko da wani suna daga sunayenSa ko wata siffa daga siffofinSa.
- AlKhaɗɗabi ya ce: Wannan yana kama da karhancin ya zama saboda cewa shi ya yi umarni a yi rantsuwa da Allah ne da kuma siffofinSa, amana kuwa ba ta daga siffofinSa, kawai ita wani al'amari ce daga aumarninSa, kuma farilla ce daga farillanSa, sai aka hanasu su rantse da ita dan abinda ke cikin hakan na daidaitawa tsakaninta da tsakanin sunayen Allah - Mai girma da ɗaukaka - da kuma siffofinSa.
Rukunan :
ILIMIN AƘIDA
· SUNAYE DA HUKUNCE-HUKUNCE
· SHIRKA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
حسبنا الله ونعم الوكيل
Allah Ya isa mana, Shi ne mafi kyawun Mai Kiyaye