Idan aka tambayi musulmi a cikin ƙabari: Yana shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Al…
Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > Idan aka tambayi musulmi a cikin ƙabari: Yana shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Al…
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Idan aka tambayi musulmi a cikin ƙabari: Yana shaidawa…
Bayanin hadisin: Idan aka tambayi musulmi a cikin ƙabari: Yana shaidawa…
Za'a tambayi mumini a cikin ƙabari, sai mala'iku biyu waɗanda aka wakilta da hakan su tambaye shi su ne Munkar da Nakir, kamar yadda ambatansu ya zo a Hadisai masu yawa, sai ya shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah , kuma cewa (Annabi) Muhammad manzon Allah ne, Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: wannan shi ne tabbatacciyar magana wacce Allah Ya faɗa a cikinta: {Allah Yana tabbatar da wadanda su ka yi imani da magana matabbaciya a rayuwar duniya da kuma a lahira} [Ibrahim: 27].
Koyarwar hadisin: Idan aka tambayi musulmi a cikin ƙabari: Yana shaidawa…
- Lallai cewa tambayar ƙabari gaskiya ne.
- Falalar Allah ga bayinSa muminai a duniya da lahira ta hanyar tabbatar da su akan tabbatacciyar magana.
- Falalar shaidawa da Tauhidi da mutuwa akan hakan.
- Tabbatar war Allah ga mumini a duniya da tabbata akan imani, da shiga hanya madaidaiciya, a lokacin mutuwa kuma da mutuwa akan Tauhidi, a ƙabari a lokacin tambayar mala'iku biyu.
Rukunan :
ILIMIN AƘIDA
· Imani da Ranar Lahira
· RAYUWAR BARZAHU
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
حسبنا الله ونعم الوكيل
Allah Ya isa mana, Shi ne mafi kyawun Mai Kiyaye