An tambayi Anas yaya karatun Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yake? …
Musulunci > Ha > Hadith > Alurani mai girma da ilimansa > An tambayi Anas yaya karatun Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yake? …
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari ne ya rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: An tambayi Anas yaya karatun Annabi - tsira da amincin…
Bayanin hadisin: An tambayi Anas yaya karatun Annabi - tsira da amincin…
An tambayi Anas ibnu Malik - Allah Ya yarda da shi - yaya karatun Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - na Alƙur'ani yake? sai ya ce: Ya kasance yana jan sautinsa da karatu ja; yana jan Lami kafin Ha'i na lafazin jalalah, kuma yana jan Mim wanda ke kafin Nun daga Al-Rahman, kuma yana jan Ha'i daga Al-Rahim.
Koyarwar hadisin: An tambayi Anas yaya karatun Annabi - tsira da amincin…
- Madda ita ce jan haruffan madda waɗanda yake sune: Alif da Wawun da kuma Ya'un, idan sun kasance masu ɗauri kuma kafinsu akwai wasalin da ya dace da su.
- Bayanin shiriyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin karatun Alƙur'ani.
- Ɗabbaƙawa na ilimi na bayanin kaifiyyar karatun Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
- Sindi ya ce: Faɗinsa: (Yana jan sautinsa ja), wato yana tsawaita haruffan da suka dace ga tsawaitawa yana neman taimako da su akan Tadabburin ma'anonin Alƙur'ani da tinani da kuma gargaɗar da wanda zai wa'azantu.
- Muhimmancin sanin Tajwidi da kuma Ulumul Ƙur'an.
- Fahimtar nassosi ana komawa ne ga malamai kawai, kamar yadda aka tambayi Anas - Allah Ya yarda da shi - sai ya bayyanawa mai tambayar.
Rukunan :
ALƘUR'ANI MAI GIRMA DA ILIMANSA
· ILIMIN TAJWIDI
· ƘIRA'AT DA TAJWIDI
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
الله أكبر
Allah Shi ne Mafi Girma