Cewa an tambayeta game da karatun Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare s…
Musulunci > Ha > Hadith > Alurani mai girma da ilimansa > Cewa an tambayeta game da karatun Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare s…
Wanda ya ruwaito hadisin: Ahmad ne ya rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Cewa an tambayeta game da karatun Manzon Allah - tsira…
Bayanin hadisin: Cewa an tambayeta game da karatun Manzon Allah - tsira…
An tambayi Nana Hafsa uwar muminai - Allah Ya yarda da ita -: Yaya Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yake karanra Alƙur'ani? Sai ta ce: Lallai ku ba zaku iya irin nasa ba, sai aka ce mata; Faɗa mana. Nafi'u ya ce sai Ibnu Abi Mulaikah ya karanta karatun da yayi shi a hankali; dan ta hakaito kuma ta kusanto musu da yadda karatun Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ke, sai ya karanta: {Alhamdu lillhi rabbil Aalamin} sannan ya yanyanke karatun, {Arrahmanur rahim}, sannan ya yanyanke karatun, {Maliki yaumid din}.
Koyarwar hadisin: Cewa an tambayeta game da karatun Manzon Allah - tsira…
- Bayanin shiriyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin karatun Alƙur'ani.
- Ɗabbaƙawa na ilimi na bayanin kaifiyyar karatun Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
- Halaccin yin karatu a hankali kuma hakan ya fi kusanto da Tadabburin ma'anoninsa.
- Himmatuwar magabata na gari da Alƙur'ani mai girma da kuma aikin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
- Muhimmancin sanin Tajwidi da kuma Ulumul Ƙur'an.
Rukunan :
ALƘUR'ANI MAI GIRMA DA ILIMANSA
· ILIMIN TAJWIDI
· ƘIRA'AT DA TAJWIDI
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
الله أكبر
Allah Shi ne Mafi Girma