Duk wanda ya halarci gawa har akai mata salla yana da kiradi guda,wanda kuma ya halarce ta…

Musulunci > Ha > Hadith > Fihu da usulu > Duk wanda ya halarci gawa har akai mata salla yana da kiradi guda,wanda kuma ya halarce ta…

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 1

Rubutun hadisin: Duk wanda ya halarci gawa har akai mata salla yana da k…

عن أبي هريرة رضي الله عنه عن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «مَنْ شهدَ الْجَنَازَةَ حتى يصلَّى عليها فله قِيرَاطٌ، ومن شهدها حتى تُدفن فله قِيرَاطان، قيل: وما القِيرَاطَانِ؟ قال: مثل الجبلين العظيمين».
ولمسلم: «أصغرهما مثل أُحُدٍ».

Bayanin hadisin: Duk wanda ya halarci gawa har akai mata salla yana da k…

Allah mai madaukakin suna da albarka mai tausasawa ne ga bayinsa, sa`annan yana nufin da ya shimfida musu dalilan yin gafara a garesu, musamman ma lokacin da zasu bar duniya, wadda ta ke ita ce gidan aiki, izuwa gidan da za`a ninke takardun ayyukan su a cikin ta. don hakanan ne ya kwadaitar bisa yin sallar jana`iza da halartar ta, saboda ita sallar neman ceto ne ga mamaci kuma tana kasancewa dalilin samun rahamar Allah. sai ya sanya ladan qiradi ga wanda ya sallace ta, ya kuma sanya wani ladan qiradin ga wanda ya halarci binne ta. wannan wani gwargwado ne daga lada mai girma kuma matsayinsa sananne ne wurin Allah madaukakin saki. yayin da gwargwadon girman wannan lada ya buya ga sahabbai Allah ya kara yarda a gare su- sai Annabi mai tsira da aminci su kara tabbata a gareshi ya kusanto da shi ga kwakwalen su, ta yadda kowane qiradi ya kai girman babban dutse; saboda abinda ke ciki na girma tsayawa akan hakkin dan uwansa musulmi tare da yin addu`ah a gareshi da tunatarwa dangane da makoma da debewa mutanen gidan kewar mamacin su da wanin haka da maslahohi.

Rukunan : FIƘHU NA IBADA · JANA'IZA · FIƘHU DA USULU · ƊAUKAR MAMACI DA BINNESHI

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 97%
Wata Sabo a cikin kwana 13
حسبنا الله ونعم الوكيل Allah Ya isa mana, Shi ne mafi kyawun Mai Kiyaye

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah