Musulunci > Ha > Hadith > Fihu na ibada > Lallai tsakanin mutum da shirka da kafirci (shi ne) barin sallah
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi gargaɗi game da barin sallar farilla, ya ba da labarin cewa tsakanin mutum da afkawa a shirka da kafirci (shi ne) barin sallah, sallah ita ce rukuni na biyu daga rukunan musulunci, al'amarinta mai girma ne a musulunci, wanda ya barta yana mai musun wajabcinta, to, ya kafirta da ijima'in musulmai, idan ya barta gabaɗaya don wulaƙantarwa da kasala, to, shi kafiri ne, an cirato ijma'in sahabbai a kan hakan, idan ya kasance yana bari wani lokaci wani lokaci kuma yana yin sallah, to, ya kai kansa ga wannan narkon mai tsanani.
Rukunan : FIƘHU NA IBADA · SALLAH · ILIMIN AƘIDA · FIƘHU DA USULU · WAJIBCIN SALLAH DA HUKUNCIN MAI BARINTA · SUNAYE DA HUKUNCE-HUKUNCE · ABUBUWAN DA SUKE WARWARE MUSULUNCI · KAFURCI