Musulmi shi ne wanda musulmai suka kubuta daga harshensa da hannunsa, wanda ya yi hijira s…
Musulunci > Ha > Hadith > Fihun halaye > Musulmi shi ne wanda musulmai suka kubuta daga harshensa da hannunsa, wanda ya yi hijira s…
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Musulmi shi ne wanda musulmai suka kubuta daga harshens…
Bayanin hadisin: Musulmi shi ne wanda musulmai suka kubuta daga harshens…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa musulmi mai cikakken Musulunci shi ne wanda musulmai suka kubuta daga harshensa ba ya zaginsu kuma ba ya la'antarsu, ba ya gulmarsu, kuma ba ya tafiya tsakaninsu da kowanne nau'i na nau'ukan cutarwa da harshensa, kuma suka kubuta daga hannunsa ba ya yi musu ta'addanci, ba ya ƙwatar dukiyoyinsu ba tare da wani haƙƙi ba, da makamantan hakan, mai hijira shi ne wanda ya bar abinda Allah - Madaukakin sarki - Ya haramta.
Koyarwar hadisin: Musulmi shi ne wanda musulmai suka kubuta daga harshens…
- Cikar Musulunci ba ya kasancewa sai da rashin cutar da wasu ta kowanne bangare.
- An kebance harshe da hannu da ambato; Dan yawan kura-kuransu da cutarsu, domin mafi girman sharruka suna bijirowa ne daga garesu.
- Kwadaitarwa akan barin sabo, da lazimtar abinda - Allah Madaukakin sarki - Ya yi umarni da shi.
- Mafificin musulmai shi ne wanda ya sauke haƙƙoƙin Allah - Madaukakin sarki - da haƙƙoƙin musulmai.
- Yin ta'addanci yakan kasance da magana ko da aiki.
- Cikakkiyar hijira ita ce kauracewa abinda Allah - Madaukakin sarki - Ya haramta.
Rukunan :
FIƘHUN HALAYE
· LADUBBA NA SHARI'A
· HALAYE NAGARI
· LADUBBAN MAGANA DA SHIRU
· ILIMIN AƘIDA
· FALALOLI DA LADUBBA
· SUNAYE DA HUKUNCE-HUKUNCE
· ƘARUWAR IMANI DA RAGUWARSA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
سبحان الله وبحمده
Tsarkin Allah da godiyarSa