Musulunci > Ha > Hadith > Falaloli da ladubba > Hakkin musulmi akan musulmi guda biyar ne: Maida sallama, da gaida mara lafiya, da bin jan…
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: «حَقُّ الْمُسْلِمِ عَلَى الْمُسْلِمِ خَمْسٌ: رَدُّ السَّلَامِ، وَعِيَادَةُ الْمَرِيضِ، وَاتِّبَاعُ الْجَنَائِزِ، وَإِجَابَةُ الدَّعْوَةِ، وَتَشْمِيتُ الْعَاطِسِ».
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana sashin hakkokin musulmi akan dan uwansa musulmi. Farkon wadannan hakkokin su ne maida sallama ga wanda ya yi maka sallama.
Hakki na biyu: Gaida mara lafiya da ziyartarsa.
Hakki na uku: Bin jana'iza daga gidansa zuwa wurin yin sallar, kuma zuwa makabarta har a binneta.
Hakki an hudu: Amsa gayyata idan ya gayyace shi zuwa walimar angwanci da wanin hakan.
Hakki na biyar: Gaida mai atishawa, shi ne ya ce masa idan ya godewa Allah: Allah ya yi maka rahama, sannana mai atishawar ya ce: Allah Ya shiryeku Ya gyara halayenku.
Rukunan : LADUBBA NA SHARI'A · LADUBBAN SALLAMA DA NEMAN IZINI · LADUBBAN ATISHAWA DA NA HAMMA · LADUBBAN DUBA MARA LAFIYA · FALALOLI DA LADUBBA