Shin kun san mece ce gibah?", suka ce: Allah da Manzonsa ne mafi sani, sai ya ce: "Ka amba…
Musulunci > Ha > Hadith > Falaloli da ladubba > Shin kun san mece ce gibah?", suka ce: Allah da Manzonsa ne mafi sani, sai ya ce: "Ka amba…
Wanda ya ruwaito hadisin: Muslim ne ya rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Shin kun san mece ce gibah?", suka ce: Allah da Manzons…
عن أبي هريرة رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «أَتَدْرُونَ مَا الْغِيبَةُ؟»، قَالُوا: اللهُ وَرَسُولُهُ أَعْلَمُ، قَالَ: «ذِكْرُكَ أَخَاكَ بِمَا يَكْرَهُ»، قِيلَ: أَفَرَأَيْتَ إِنْ كَانَ فِي أَخِي مَا أَقُولُ؟ قَالَ: «إِنْ كَانَ فِيهِ مَا تَقُولُ فَقَدِ اغْتَبْتَهُ، وَإِنْ لَمْ يَكُنْ فِيهِ فَقَدْ بَهَتَّهُ».
Bayanin hadisin: Shin kun san mece ce gibah?", suka ce: Allah da Manzons…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayyana haƙiƙanin gibar da aka haramta, ita ce: Ambaton musulmi mai gibar da abin da yake ki, daidai ne ya kasance daga siffofinsa ne na halitta ko na ɗabi'a, kamar: Mai ido ɗaya mai yawan algus maƙaryaci, da makamancin hakan daga siffofin zargi, ko da waɗannan siffofin sun kasance samammu ne a gareshi.
Amma idan babu siffar a tare da shi, to, wannan ya fi tsanani daga giba, shi ne ƙirƙirar ƙarya, wato: Ƙirkirar abin da babu a tare da shi.
Koyarwar hadisin: Shin kun san mece ce gibah?", suka ce: Allah da Manzons…
- Kyakkyawar koyarwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ta inda yake jefa mas'aloli ta hanyar tambaya.
- Kyakkyawan ladabin sahabbai tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yayin da suka ce: Allah da Manzonsa ne mafi sani.
- Faɗin wanda aka tamabaya abin da bai sanshi ba; Allah ne mafi sani.
- Karewar shari'a ga zamatakewa ta hanyar kare haƙƙoƙi da 'yan uwantaka a tsakaninsu.
- Giba abar haramtawa ce sai a wasu halaye dan maslaha; daga hakan akwai: Tunkuɗe zalunci, ta yadda wanda aka zalunta zai ambaci wanda ya zalunceshi ga wanda zai iya karɓa masa haƙƙinsa, sai ya ce: Wane ya zalunceni, ko ya yi min kaza, daga ciki akwai: Shawara a al'amarin aure ko tarayya ko maƙotaka, da makancin hakan.
Rukunan :
LADUBBA NA SHARI'A
· LADUBBAN MAGANA DA SHIRU
· FALALOLI DA LADUBBA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
سبحان الله وبحمده
Tsarkin Allah da godiyarSa