Idan ɗayanku ya haɗu da ɗan uwansa to ya yi masa sallama, idan bishiya ko katanga ko duts…
Musulunci > Ha > Hadith > Ladubba na sharia > Idan ɗayanku ya haɗu da ɗan uwansa to ya yi masa sallama, idan bishiya ko katanga ko duts…
Wanda ya ruwaito hadisin: Abu Dawud ne Ya Rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Idan ɗayanku ya haɗu da ɗan uwansa to ya yi masa salla…
Bayanin hadisin: Idan ɗayanku ya haɗu da ɗan uwansa to ya yi masa salla…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kwaɗaitar da musulmi da yin sallama ga ɗan uwansa musulmi duk lokacin da ya haɗu da shi, koda sun kasance suna tafiya tare ne kuma wani abu mai rabawa ya raba su, kamar bishiya ko gini ko babban dutse, sannan ya haɗu da shi bayan nan to ya yi masa sallama karo na biyu.
Koyarwar hadisin: Idan ɗayanku ya haɗu da ɗan uwansa to ya yi masa salla…
- An so yaɗa sallama, kuma a maimaitata a lokacin canjin hali.
- Tsananin kwaɗayinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - akan yaɗa sunnar sallama da kai matuƙa a cikinta; dan abinda ke cikinta na jawo soyayya da hada tsakanin musulmai.
- Sallama ita ce faɗin: Assalamu alaikum, (Aminci ya tabbata a gareku) ko: Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh, wato(Aminci ya tabbata a gareku da rahamar Allah da albarkarSa), banda musafahar da take faruwa alokacin farkon haɗuwa.
- Sallama addu'a ce, musulmai suna cikin buƙatuwar junansu su yi wa junansu addu'a koda hakan ya maimaitu.
Rukunan :
LADUBBA NA SHARI'A
· LADUBBAN SALLAMA DA NEMAN IZINI
· FALALOLI DA LADUBBA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
الله أكبر
Allah Shi ne Mafi Girma