An umurce ni da in yaki mutane har sai sun shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Al…

Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > An umurce ni da in yaki mutane har sai sun shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Al…

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 1

Rubutun hadisin: An umurce ni da in yaki mutane har sai sun shaida cewa…

عَنِ ابْنِ عُمَرَ رضي الله عنهما أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «أُمِرْتُ أَنْ أُقَاتِلَ النَّاسَ حَتَّى يَشْهَدُوا أَنْ لاَ إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ، وَأَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اللَّهِ، وَيُقِيمُوا الصَّلاَةَ، وَيُؤْتُوا الزَّكَاةَ، فَإِذَا فَعَلُوا ذَلِكَ عَصَمُوا مِنِّي دِمَاءَهُمْ وَأَمْوَالَهُمْ إِلَّا بِحَقِّ الإِسْلاَمِ، وَحِسَابُهُمْ عَلَى اللَّهِ».

Bayanin hadisin: An umurce ni da in yaki mutane har sai sun shaida cewa…

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa Allah Ya umarce shi da yakar mushrikai har sai sun shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai ba Shi da abokin tarayya, kuma su shaida manzanci ga (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, da aiki da abinda wannan shaidar ta hukunta na kiyayewa akan salloli biyar a yini da dare, kuma su bada zakka ta wajibi ga wadanda suka cancanta. Idan suka aikata wadannan al'amuran to Musulunci ya tsare jinanensu da dukiyoyinsu, kashe su ba ya halatta sai dai idan sun aikata laifi ko wata barnar da za su cancanci kisa akanta, ta hanyar wajabcin hukunce-hukuncen Musulunci, sannan ranar AlKiyama Allah - Madaukakin sarki - Zai jibinci hisabunsu inda Yake sanin sirrikansu.

Koyarwar hadisin: An umurce ni da in yaki mutane har sai sun shaida cewa…

Rukunan : ILIMIN AƘIDA · SUNAYE DA HUKUNCE-HUKUNCE · MUSULUNCI

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
حسبنا الله ونعم الوكيل Allah Ya isa mana, Shi ne mafi kyawun Mai Kiyaye

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah