Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > Wanda ya ga wani mummunan abu daga cikinku, to ya canza shi da hannunsa, idan ba zai iya …
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1عن أبي سعيد الخُدْريِّ رضي الله عنه قال: سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: «مَنْ رَأَى مِنْكُمْ مُنْكَرًا فَلْيُغَيِّرْهُ بِيَدِهِ، فَإِنْ لَمْ يَسْتَطِعْ فَبِلِسَانِهِ، فَإِنْ لَمْ يَسْتَطِعْ فَبِقَلْبِهِ، وَذَلِكَ أَضْعَفُ الْإِيمَانِ».
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana yin umarni da canza abin ki - wanda shi ne dukkanin abinda Allah da ManzonSa suka hana - gwargwadon iko, Idan ya ga wani abin ki to yana wajaba akansa ya canja shi da hannu idan yana da iko, Idan ya gajiya akan hakan, to ya canja shi da harshensa, ta hanyar hana mai aikatawar, kuma ya bayyana masa cutar hakan, ya kuma shiryar da shi zuwa alheri maimakon wannan sharrin, Idan ya gajiya daga wannan matakin, to ya canja shi da zuciyarsa shi ne ya ki wannan mummunan aikin, kuma ya yi niyyar cewa shi da yana da iko akan canja shi to da ya aikata, canzawa da zuciya shi ne mafi raunin matakan imani a canja abin ki.
Rukunan : ILIMIN AƘIDA · UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DAGA MUMMUNA · HUKUNCIN UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DAGA MUMMUNA · Principles of Enjoining Good and Forbidding Evil · DA'AWA DA HISBA · SUNAYE DA HUKUNCE-HUKUNCE · ƘARUWAR IMANI DA RAGUWARSA