Musulunci > Ha > Hadith > Fihu da usulu > Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sanar dani Tahiya, tafukan…
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 2عَنِ ابْنَ مَسْعُودٍ رضي الله عنه قَالَ: عَلَّمَنِي رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، وَكَفِّي بَيْنَ كَفَّيْهِ، التَّشَهُّدَ، كَمَا يُعَلِّمُنِي السُّورَةَ مِنَ القُرْآنِ: «التَّحِيَّاتُ لِلَّهِ، وَالصَّلَوَاتُ وَالطَّيِّبَاتُ، السَّلاَمُ عَلَيْكَ أَيُّهَا النَّبِيُّ وَرَحْمَةُ اللَّهِ وَبَرَكَاتُهُ، السَّلاَمُ عَلَيْنَا وَعَلَى عِبَادِ اللَّهِ الصَّالِحِينَ، أَشْهَدُ أَنْ لاَ إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ، وَأَشْهَدُ أَنَّ مُحَمَّدًا عَبْدُهُ وَرَسُولُهُ».
وفي لفظ لهما: «إِنَّ اللهَ هُوَ السَّلَامُ، فَإِذَا قَعَدَ أَحَدُكُمْ فِي الصَّلَاةِ فَلْيَقُلْ: التَّحِيَّاتُ لِلَّهِ وَالصَّلَوَاتُ وَالطَّيِّبَاتُ السَّلَامُ عَلَيْكَ أَيُّهَا النَّبِيُّ وَرَحْمَةُ اللهِ وَبَرَكَاتُهُ، السَّلَامُ عَلَيْنَا وَعَلَى عِبَادِ اللهِ الصَّالِحِينَ، فَإِذَا قَالَهَا أَصَابَتْ كُلَّ عَبْدٍ لِلَّهِ صَالِحٍ فِي السَّمَاءِ وَالْأَرْضِ، أَشْهَدُ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ، وَأَشْهَدُ أَنَّ مُحَمَّدًا عَبْدُهُ وَرَسُولُهُ، ثُمَّ يَتَخَيَّرُ مِنَ الْمَسْأَلَةِ مَا شَاءَ».
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sanar da Dan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - Tahiyar da ake fada a cikin sallah, hakika ya sanya hannunsa a cikin hannayensa, dan ya karkato da hankalin Dan Mas'ud gare shi, kamar yadda yake sanar da shi sura daga Alkur’ani abinda yake nuni akan kulawar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da wannan Tahiyar lafazi da ma'ana. Sai ya ce: "(Tsarkakan) Gaisuwa sun tabbata ga Allah": Su ne kowacce magana ko aiki mai shirayrwa akan girmamawa, dukkaninsu ababen cancantane ga Allah - Mai girma da daukaka -. "Salloli": Ita ce sananniyar sallah ta farilla da ta nafila, sun tabbata ga Allah - Madaukakin sarki -. "Tsarkakan Maganganu": Su ne maganganu da ayyuka da siffofi tsarkaka masu nuni akan cika, dukkaninsu ababen cancanta ne ga Allah - Madaukakin sarki -. "Aminci ya tabbata agareka Ya kai wannan Annabi da rahamar Allah da albarkarSa': Addu'ace gare shi da aminta daga dukkanin cututtuka da abin ki, da kari da yawaita a kowanne alheri. "Aminci ya tabbata agaremu da bayin Allah na gari": Addu'ace da aminta daga mai sallah da kuma kowanne bawa na gari a sama da kasa. "Ina shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah': Wato ina tabbatarwa tabbatarwa a yanke cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah. "Kuma cewa Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne": Ina tabbatarwa a gare shi da bauta da Manzanci na karshe.
Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwadaitar da mai yin sallah ya zabi abinda yaso na addu'a ya roka.
Rukunan : FIƘHU NA IBADA · SALLAH · FIƘHU DA USULU · SIFFAR SALLAH