Musulunci > Ha > Hadith > Fihu da usulu > Naga Manzon Allah tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yanazaune ya tanqwashe Qafa…
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1عن عائشة رضي الله عنها قالت: رأيت رسول الله صلى الله عليه وسلم يصلِّي متربِّعًا.
Tarabbu'e: Zhi ne ya sanya cikin tafin kafarsa a qarqashin cinyarsa ta Hagu, kuma cikin Hagunsa a qarqashin cinyar Dama, kuma ya zauna akan Mazaunansa, kuma haqiqa Manzon Allah SAW wannan yayin da ya faxo ne daga kan Dokinsa, kuma kuma yayi targaxe a Qafarsa, to idan mai sallah ya gajiya ga barin tsayuwa to yayi Sallah a zaune Mustahabi ne, kuma wannan a cikin Halin zamansa a maimakon tsayuwa, amma a lokacin zamansa a tsakani Sujadodi guda biyu, da zamansa a tsakani tahiya guda biyu, da zamansa a tsakanin tahiyoyi guda biyu, to an so ya zauna yana Mai zaman Iftirash a tahiyar farko, da kuma zaman Tawarruk a tahiya ta Biyu, kuma dukkan waxan nan Siffofin suna daga cikin babin Mustahabanci da kuma fifiko, da ace zai sava kuma ya zauna akan wata kamar ba wannan ba to da ya isar masa; saboda abun nema shi ne zaman domin Tahiyar kuma waxan Siffofi gwargwado ne na Wajibi
Rukunan : FIƘHU NA IBADA · SALLAH · FIƘHU DA USULU · SALLAR MASU UZURI