Musulunci > Ha > Hadith > Fihu da usulu > na kwana a wajan Gwaggwona Maimuna,sai Manzan Allah ya tashi yana salla da daddare,sai na …
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1عن عَبدُ اللَّهِ بنِ عَبَّاسٍ رضي الله عنهما قال: «بِتُّ عِندَ خَالَتِي مَيمُونَة، فَقَام النَبيَّ صلى الله عليه وسلم يُصَلِّي مِن اللَّيل، فَقُمتُ عَن يَسَارِه، فَأَخَذ بِرَأسِي فَأَقَامَنِي عن يَمِينِه».
Sahabi maigirma dan Abbas Allah ya yarda dasu ya bada labari cewa ya kwana a wajan Gwaggwonsa matar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, don yai tsinkayi da kansa yadda tsayuwar daren Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi take yayin da Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya tashi da daddare, sai dan Abbas ya tashi don yai salla tare dashi, sai ya zama a hagun Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi a matsayin mamu;saboda cewa dama ita tafi kuma itace wajan tsayuwar mamu daga liman in ya kasance shi kadai ne sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya ruko kansa, ya jawo shi ta bayansa,sai ya tsayar dashi a damansa
Rukunan : FIƘHU NA IBADA · SALLAH · FIƘHU DA USULU · SALLAR NAFILA · TSAYUWAR DARE