Lallai ba'a karvar ran wani Annabi face sai an nuna masa Masaukinsa a Al-janna, sannan a b…

Musulunci > Ha > Hadith > Sira da tarihi > Lallai ba'a karvar ran wani Annabi face sai an nuna masa Masaukinsa a Al-janna, sannan a b…

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 1

Rubutun hadisin: Lallai ba'a karvar ran wani Annabi face sai an nuna mas…

عن عائشة قالت: كان النبي صلى الله عليه وسلم يقول وهو صحيح: «إنَّه لم يُقبض نبيٌّ حتى يرى مقعدَه من الجنة، ثم يُخَيَّر» فلمَّا نزل به، ورأسه على فخِذي غُشِي عليه، ثم أفاق فأشْخَصَ بصرَه إلى سقف البيت، ثم قال: «اللهمَّ الرَّفِيقَ الأعلى». فقلتُ: إذًا لا يختارنا، وعرفتُ أنَّه الحديثُ الذي كان يحدِّثنا وهو صحيح، قالت: فكانت آخر كلمة تكلَّم بها: «اللهمَّ الرَّفِيقَ الأعلى».

Bayanin hadisin: Lallai ba'a karvar ran wani Annabi face sai an nuna mas…

Nana Aisha -Allah ya yarda da ita- tana cewa: Manzon Allah ya kasance a lokacin yanada lafiya yana cewa kafin yayi rashin lafiyar Mutuwarsa: cewa babu wani Annabi da zai Mutu daga cikin Annabawa har sai Allah ya nuna masa Mahallinsa a Aljanna, sannan ya bashi zavin zama a Duniya ko kuma ya xaukeshi zuwa Masaukinsa a Aljanna, Aisha ta ce: yayin da manzon Allah SAW yayi rashin lafiyar Mutuwarsa, kansa yana kan cinya ta, sai ya suma sannan ya farka, sai ya xaga kansa zuwa rufin xakin sannan ya ce: "Ya Ubangiji zuwa Makwabtaka Maxaukakiya" ai ya zavi kusanci su ne Jama'ar Annabawa waxanda suke zaune a sama sama, Nana Aisha ta ce idan Allah ya bashi zavin tsakanin Duniya da Lahira to shi zai zavi Lahira ne, ba zai zave mu ba, kuma nasan cewa wannan zavin shi ne zancen da yake gaya mana lokacin yana lafiya, Aisha ta ce: Qarshen kalmar da ya faxa SAW ita ce: "Ya Ubangiji zuwa Makwabtaka Maxaukakiya"

Rukunan : SIRAR ANNABI · WAFATINSA TSIRA DA AMINCIN SU TABBATA A GARESHI · SIRA DA TARIHI

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
لا حول ولا قوة إلا بالله Babu wata ƙarfi ko iko sai na Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah