Musulunci > Ha > Hadith > Daawa da hisba > Babu wani bawa da Allah Zai ba shi kulawar wani abin kiwo, ya mutu a ranar da zai mutu alh…
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1عن مَعقِلِ بن يَسار المُزَنِيّ رضي الله عنه قال: إني سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: «مَا مِنْ عَبْدٍ يَسْتَرْعِيهِ اللهُ رَعِيَّةً، يَمُوتُ يَوْمَ يَمُوتُ وَهُوَ غَاشٌّ لِرَعِيَّتِهِ، إِلَّا حَرَّمَ اللهُ عَلَيْهِ الْجَنَّةَ».
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbat a gareshi - yana ba da labarin cewa kowane mutumin da Allah - Maɗaukakin sarki - Ya sanyashi majiɓinci, kuma shugaba ga mutane, duk ɗaya ne ya kasance shugabanci ne mai gamewa kamar sarki, ko keɓantaccen shugabanci ne kamar mutum a gidansa da mace a gidanta, sai ya gaza a haƙƙin waɗanda aka ba shi kiwonsu, ya yi musu algus bai yi musu nasiha ba, sai ya tozarta haƙƙoƙinsu na addini da na duniya, to, haƙiƙa ya cancanci wannan uƙubar mai tsanani.
Rukunan : SIYASA A SHARI'ANCE · DA'AWA DA HISBA