Duk wanda ya fita daga biyayya, ya kuma rabu da jama'a sai ya mutu, to, ya mutu irin mutuw…

Musulunci > Ha > Hadith > Siyasa a shariance > Duk wanda ya fita daga biyayya, ya kuma rabu da jama'a sai ya mutu, to, ya mutu irin mutuw…

Wanda ya ruwaito hadisin: Muslim ne ya rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Duk wanda ya fita daga biyayya, ya kuma rabu da jama'a…

Bayanin hadisin: Duk wanda ya fita daga biyayya, ya kuma rabu da jama'a…

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa wanda ya fita daga biyayyar majiɓinta al'amura, kuma ya rabu da jama'ar musulunci wacce ta haɗu a kan caffar (mubaya’a) shugaba, sai ya mutu a kan wannan halin na rabuwa da rashin biyayya, to, ya mutu irin mutuwar 'yan Jahiliyya, waɗanda ba sa bin wani shugaba, kuma ba sa tarowa zuwa jama'a ɗaya, kawai sun kasance ƙungiyoyi da jama'a-jama'a da sashinsu yana yaƙar sashi.

(Annabi) Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ba da labarin cewa wanda ya yi yaƙi ƙarƙashin tutar da ba a fayyace gaskiyarta daga ƙaryarta ba, yana fushi saboda tsantsar ƙanilanci ga mutanensa ko ƙabilarsa, ba don taimakon Addini ko gaskiya ba, sai ya yi yaƙi don ƙabilanci ba tare da basira ko ilimi ba, to, idan aka kasheshi a kan wannan halin, ya zama kamar kisan Jahiliyya.

Kuma wanda ya yi fito na fito da al'ummarsa (Annabi) - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yake dukan mutumin kirkinta da fajirinta, ba ya kulawa da abin da yake aikatawa kuma ba ya jin tsoron uƙubarsa na kashe mumininta, kuma ba ya cika alƙawari ga ma'abota alƙawari daga cikin kafirai ko majiɓinta al'amura sai dai ma yana warwaresu, to, wannan yana daga manyan zunubai, wanda ya aikata shi, to, haƙiƙa ya cancanci wannan narkon mai tsanani.

Koyarwar hadisin: Duk wanda ya fita daga biyayya, ya kuma rabu da jama'a…

Rukunan : SIYASA A SHARI'ANCE · YI WA SHUGABA TAWAYE · DA'AWA DA HISBA

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
حسبنا الله ونعم الوكيل Allah Ya isa mana, Shi ne mafi kyawun Mai Kiyaye

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah