Lallai za'a samu wasu shugabanni zasu dinga ƙarya suna zalinci, wanda ya gasgata su akan ƙ…
Musulunci > Ha > Hadith > Umarni da kyakkyawa da hani daga mummuna > Lallai za'a samu wasu shugabanni zasu dinga ƙarya suna zalinci, wanda ya gasgata su akan ƙ…
Wanda ya ruwaito hadisin: Ahmad ne ya rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Lallai za'a samu wasu shugabanni zasu dinga ƙarya suna…
Bayanin hadisin: Lallai za'a samu wasu shugabanni zasu dinga ƙarya suna…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wasu shagabanni da zasu shugabanci mutane bayan rasuwarsa zasu dinga ƙarya a magana sai su dinga faɗin abinda ba sa aikatawa, kuma suna zalinci a cikin hukunci, wanda ya shiga gurinsu ya gasgata su akan ƙaryarsu, kuma ya taimakesu da aikata zalinci ko faɗarsa, kamar ba su fatawa dan neman kusancinsu da kwaɗayin abinda ke hannunsu; to ni babu ruwana da shi, ba shi ba ni, ba ni ba shi, kuma ba zai zo Alkausara ba ranar alƙiyama. Wanda bai shige su ba , kuma bai gasgatasu akan ƙaryarsu ba kuma bai taimakesu akan zalincinsu ba to yana tare da ni, kuma zai zo Alkausara ranar alƙiyama ba.
Koyarwar hadisin: Lallai za'a samu wasu shugabanni zasu dinga ƙarya suna…
- Shugabanni idan an shiga gurinsu dan fadakarwa da shiryarwa da sauƙaƙa sharri; wannan shi ne abin nema, amma idan ya shiga gurinsu dan ya taimakesu akan zalinci kuma ya gasgatasu da ƙarya to wannan shi ne abin zargi.
- Bayanin narko na azaba ga wanda ya taimaki wani shugaba akan zalincinsa.
- Wannan narkon a cikin Hadisin yana nuni akan haramcin wannan aikin, kuma hakan yana daga cikin manyan zunubai.
- Kwaɗaitarwa a kan taimakekeniya akan aikin alheri da kuma tsoron Allah, da rashin taimakekeniya a kan zunubi da shisshigi.
- Tabbatar da tafkin Alkausara ga Annabinmu Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, kuma lallai cewa al'ummarsa zasu gangaro zuwa gare shi.
Rukunan :
UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DAGA MUMMUNA
· SIYASA A SHARI'ANCE
· LADUBBAN UMARNI DA KYAKKYAWAN AIKI DA HANI DAGA MUMMUNA
· HAƘƘIN SHUGABA A KAN MABIYA
· DA'AWA DA HISBA
بسم الله الرحمن الرحيم
Lar 16 Jumada al-Awwal
الأربعاء 16 جمادى الأولى
لا إله إلا الله
Babu abin bautawa sai Allah