Ina yi muku wasicci da jin tsoron Allah, da ji da bi, ko da bawa ne ya shugabance ku, domi…

Musulunci > Ha > Hadith > Hadisi da ilimansa > Ina yi muku wasicci da jin tsoron Allah, da ji da bi, ko da bawa ne ya shugabance ku, domi…

Wanda ya ruwaito hadisin: Abu Dawud da Tirmizi ne Suka Rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Ina yi muku wasicci da jin tsoron Allah, da ji da bi, k…

عَنْ أَبِي نَجِيحٍ العِرْبَاضِ بْنِ سَارِيَةَ رضي الله عنه قَالَ: وَعَظَنَا رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ مَوْعِظَةً وَجِلَتْ مِنْهَا القُلُوبُ، وَذَرَفَتْ مِنْهَا العُيُونُ، فَقُلْنَا: يَا رَسُولَ اللهِ! كَأَنَّهَا مَوْعِظَةُ مُوَدِّعٍ؛ فَأَوْصِنَا، قَالَ: «أُوصِيكُمْ بِتَقْوَى اللَّهِ، وَالسَّمْعِ وَالطَّاعَةِ، وَإِنْ تَأَمَّرَ عَلَيْكُمْ عَبْدٌ، فَإِنَّهُ مَنْ يَعِشْ مِنْكُمْ بَعْدِي فَسَيَرَى اخْتِلَافًا كَثِيرًا، فَعَلَيْكُمْ بِسُنَّتِي وَسُنَّةِ الخُلَفَاءِ الرَّاشِدِينَ المَهْدِيينَ، عَضُّوا عَلَيْهَا بِالنَّوَاجِذِ، وَإِيَّاكُمْ وَمُحْدَثَاتِ الأُمُورِ؛ فَإِنَّ كُلَّ بِدْعَةٍ ضَلَالَةٌ».

Bayanin hadisin: Ina yi muku wasicci da jin tsoron Allah, da ji da bi, k…

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa sahabbansa wa'azi wa'azi isasshe zukata sun ji tsoro daga gare shi, kuma idanuwa sun zubar da hawaye daga gare shi, Sai suka ce : Ya Manzon Allah ! kai ka ce wannan wa'azin bankwana ne, saboda abinda suka gani ya kai matukarsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a wa'azi, sai suka nemi wata wasiyyar dan su yi riko da ita a bayansa, Ya ce: Ina yi muku wasicci da tsoron Allah - Mai girma da daukaka -, hakan da aikata wajibai da barin abubuwan da aka haramta, da ji da bi, wato: Ga shugabanni, koda bawa ne ya shugabanceku ko ya yi rinjaye a kanku, wato ya zama mafi kaskantar halitta sarki akanku kada ku hanu daga hakan, ku bi shi dan tsoron tada fitintinu, domin shi wanda ya rayu daga cikinku zai ga sabani mai yawa. Sannan ya bayyana musu mafita daga wannan sabanin, hakan dayin riko da sunnarsa da sunnar Halifofi shiryayyu a bayansa, Abu bakar Al-Siddik, da Umar Dan Al-khaddab, da Usman Dan Affan, da Aliyu Dan Abu Dalib - Allah Ya yarda su baki daya -, da riketa da turamen hakora wato - turamen hakora na karshe -: Yana nufi da hakan kokari a lazimtar sunna da yin riko da ita, ya kuma gargadesu daga fararrun al'amura kirkirarru a Addini, domin cewa kowacce bidi'a bata ce.

Koyarwar hadisin: Ina yi muku wasicci da jin tsoron Allah, da ji da bi, k…

Rukunan : FALALAR SAHABBAI · HADISI DA ILIMANSA · ILIMIN AƘIDA · SIYASA A SHARI'ANCE · HAƘƘIN SHUGABA A KAN MABIYA · BINCIKE-BINCIKE GAMAMMU CIKIN SUNNA · MUHIMMANCIN SUNNA DA MATSAYINTA · DA'AWA DA HISBA · SAHABBAI

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
لا حول ولا قوة إلا بالله Babu wata ƙarfi ko iko sai na Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah