Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > Wanda ya rantse da wanin Allah to hakika ya kafirta ko ya yi shirka
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1عن ابْنِ عُمَرَ رضي الله عنهما أنه سَمِعَ رَجُلًا يَقُولُ: لَا وَالْكَعْبَةِ، فَقَالَ ابْنُ عُمَرَ: لَا يُحْلَفُ بِغَيْرِ اللَّهِ، فَإِنِّي سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «مَنْ حَلَفَ بِغَيْرِ اللهِ فَقَدْ كَفَرَ أَوْ أَشْرَكَ».
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bada labarin cewa wanda ya yi rantsuwa da wanin Allah da sunayensa da siffofinsa to hakika ya kafircewa Allah ko ya yi shirka; domin rantsuwa tana hukunta girmama wanda aka rantse da shi, girma kadai ya tabbata ga Allah ne Shi kadai; ba'a rantsuwa sai da Allah da sunayensa da siffofinsa - tsarki ya tabbatar masa, Wannan rantsuwar tana daga karamar shirka; saidai da a ce mai rantsuwa ya girmama abinda ya rantse da shi kamar girmama Allah - Madaukakin sarki - ko sama da haka; to a wannan lokacin zai zama daga babbar shirka.
Rukunan : ILIMIN AƘIDA · SUNAYE DA HUKUNCE-HUKUNCE · SHIRKA