Wanda ya farar da (wani abu) daga cikin al'amarinmu wannan abinda ba ya ciknsa to an mayar…
Musulunci > Ha > Hadith > Ilimin aida > Wanda ya farar da (wani abu) daga cikin al'amarinmu wannan abinda ba ya ciknsa to an mayar…
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Wanda ya farar da (wani abu) daga cikin al'amarinmu wan…
عَنْ عَائِشَةَ رضي الله عنها قَالَتْ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صلى الله عليه وسلم: «مَنْ أَحْدَثَ فِي أَمْرِنَا هَذَا مَا لَيْسَ فِيهِ فَهُوَ رَدٌّ» متفق عليه.
ولمسلم: «مَنْ عَمِلَ عَمَلًا لَيْسَ عَلَيْهِ أَمْرُنَا فَهُوَ رَدٌّ».
Bayanin hadisin: Wanda ya farar da (wani abu) daga cikin al'amarinmu wan…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa wanda ya yi kirkira a Addini ko ya aikata wani aikin da wani dalili bai yi nuni akansa ba na Alkur’ani ko hadisi, to shi abin juyarwane akan mai shi ba abin karba ba ne a wurin Allah.
Koyarwar hadisin: Wanda ya farar da (wani abu) daga cikin al'amarinmu wan…
- Ibadu an gina su ne akan abinda ya zo ne kawai a cikin Alkur’ani da sunna, ba zamu bautawa Allah - Madaukakin sarki - ba sai da abinda Ya shara'anta ba da bidi'o'i ko kirkirarrun abubuwa ba.
- Addini ba ra'ayi ba ne, ko ganin kyan abu, kadai da bin Manzon Allah ne - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
- Wannan hadisin dalili ne akan cikar Addini.
- Bidi'a ita ce dukkanin abinda aka farar a Addini wanda babu shi a lokacin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi, da sahabbansa na akida ne ko magana ko aiki.
- Wannan Hadisin tushe ne daga tushen Musulunci, shi kamar ma'auni ne ga ayyuka, kamar yadda kowanne aikin da ba'a nufi zatin Allah - madaukakin sarki - da shi ba, to mai aikata shi ba shi da wani lada, hakanan kowanne aikin da bai zama ya dace da abinda Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo da shi ba to shi abin juyarwa ne akan mai aikata shi.
- Fararrun abubuwan da aka hana su ne abinda suka kasance na al'amuran Addini, ba na duniya ba.
Rukunan :
BIDI'A
· ILIMIN AƘIDA
· SUNAYE DA HUKUNCE-HUKUNCE
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
الله أكبر
Allah Shi ne Mafi Girma