Musulunci > Ha > Hadith > Fihu na ibada > Dabi'a (ta addinin Musulunci ) guda biyar ce: Kaciya da aske gashin mara, da rage gashin b…
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana ɗabi'u biyar daga addinin Musulunci da kuma sunnonin manzanni:
Na farkonsu: Kaciya, ita ce yanke fatar da ta ƙaru a kan azzakari wajen kan kaciya, da kuma yanke kan fata a farjin mace a saman bigiren mashigar azzakari.
Na biyunsu: Aske gashin mara, shi ne aske gashin mara wanda ke gefen gaba.
Na ukunsu: Rage gashin baki, shi ne rage abin da ya tsiro a kan leɓen sama na namiji inda leɓe yake bayyana.
Na huɗunsu: Yanke farata.
Na biyar ɗinsu: Aske gashin hammata.
Rukunan : FIƘHU NA IBADA · TSARKI · FIƘHU DA USULU · SUNNONIN FITRA