Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance damantawa tana kayatar …
Musulunci > Ha > Hadith > Sirar annabi > Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance damantawa tana kayatar …
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -…
Bayanin hadisin: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana so kuma yana fifita cewa ya fara da dama a al'amuransa masu dacewa da girmamawa, daga cikin hakan: Ya fara da kafar dama a sanya takalminsa, kuma yana farawa da dama a taje gashin kansa da gemunsa a tajesu da shafa musu mai, a alwalarsa kuma yana gabatar da dama akan hagu daga hannaye da kafafuwa.
Koyarwar hadisin: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -…
- Nawawi ya ce: Wannan ka'ida ce tabbatacciya a shari'a, ita ce: cewa abinda ya kasance daga babin giramamawa da daukaka, kamar sanya tufa da wanduna da huffi da shiga masallaci da asuwaki da sanya kwalli, da yanke farce, da rage gashin baki, da taje kai shi ne yi masa kum, da cire gashin hammata, da aske kai, da sallama daga sallah, da wanke gabban alwala, da fita daga bandaki, da ci da sha, da musafaha, da sumbatar (Alhajarul Aswad) bakin dutse, da wanin hakan na abinda yake a cikin ma'anarsa anso damantawa a cikinsa. Amma abinda ya kasance kishiyarsa kamar shiga bandaki, da fita daga masallaci da face majina, da tsarki, da tube tufafi da wanduna da huffi da abinda ke kama da hakan, to an so haguntawa a cikinsa, wannan saboda girmama dama da kuma daukakarta.
- "Damantawa yana kayatar da shi". Ya kunshi: Farawa a cikin ayyuka da hannun dama, da kafar dama, da bangaren dama, da bada abu da dama.
- Nawawi ya ce: Ka sani cewa daga gabban alwala a kwai wadanda ba’a son damantawa a cikinsu; shi ne kunnuwa da tafuka da kundukuki kai za'a tsarkakesu ne karo daya, idan hakan ya wuyata kamar a hakkin mai dungu da makamancinsa; sai a gabatar da dama.
Rukunan :
SIRAR ANNABI
· ƊABI'U IRIN NA (ANNABI) MUHAMMAD
· TUFAFINSA (MANZON ALLAH) TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARESHI
· TSARIN ANNABI
· SIRA DA TARIHI
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
الله أكبر
Allah Shi ne Mafi Girma