Na tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da gani na fu…
Musulunci > Ha > Hadith > Abubuwa masu tausasa zukata da waazozi > Na tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da gani na fu…
Wanda ya ruwaito hadisin: Muslim ne ya rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Na tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tab…
Bayanin hadisin: Na tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tab…
Jarir ɗan Abdullahi - Allah Ya yarda da shi - ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da ganin da namiji zai yi wa mace manisanciyarsa bagtatan ba tare da nufi ba? sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarce shi cewa ya wajaba agare shi ya juyar da fuskarsa zuwa wani ɓangaren da wata nahiyar daban da zarar ya sani, babu laifi akansa.
Koyarwar hadisin: Na tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tab…
- Kwaɗaitarwa akan rintse ido.
- Gargaɗi akan dawwamar da gani akan abinda yake haramta gare shi, idan ganinsa ya afku bagatatan kuma ba tare da nufi ba.
- A cikinsa kuma akwai haramcin duba zuwa ga mace wani al’amari ne tabbatacce a gurin sahabbai saboda dalilin cewa Jarir - Allah Ya yarda da shi - ya tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - daga abinda da ganinsa ya afka akan wata mace ba tare da nufi ba, shin hukuncinsa hukuncin wanda ya yi nufin gani ne?
- A cikinsa akwai kulawar shari'a ga maslahohin bayi, cewa ita ta haramta musu kallo zuwa ga mata saboda abinda yake biyo baya akansa na ɓarna iri daban daban na duniya da lahira.
- Komawar sahabbai zuwa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da tambayarsa game da abinda yake rikitar da su, haka nan yana kamata ga kowa da kowa komawa zuwa ga malumansu da tambayarsu game da abinda ya rikitar da su.
Rukunan :
ABUBUWA MASU TAUSASA ZUKATA DA WA'AZOZI
· TSARKAKE ZUKATA
· FALALOLI DA LADUBBA
بسم الله الرحمن الرحيم
Lar 16 Jumada al-Awwal
الأربعاء 16 جمادى الأولى
الحمد لله
Alhamdulillah - Godiya ta tabbata ga Allah