Idan bawa musulmi ya yi alwala - ko kuma mumini - sai ya wanke fuskar sa, to kowane kuskur…
Musulunci > Ha > Hadith > Fihu na ibada > Idan bawa musulmi ya yi alwala - ko kuma mumini - sai ya wanke fuskar sa, to kowane kuskur…
Wanda ya ruwaito hadisin: Muslim ne ya rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Idan bawa musulmi ya yi alwala - ko kuma mumini - sai y…
Bayanin hadisin: Idan bawa musulmi ya yi alwala - ko kuma mumini - sai y…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa idan musulmi ko mumini ya yi alwala sai ya wanke fuskarsa a cikin alwalar duk ƙaramin kuskuren da ya kalla da idanuwansa zai fita daga fuskarsa tare da ruwan da ya zuba bayan wankewar ko tare da ƙarshen ɗigon ruwan, idan ya wanke hannayensa kowane ƙaramin kuskuren da hannayensa suka aikata shi zai fita daga hannayensa tare da ruwan ko tare da ƙarshen ɗigon ruwan, idan ya wanke ƙafafuwansa kowane ƙaramin kuskuren da ƙafafuwansa suka taka (zuwa gare shi) zai fita tare da ruwan ko tare da ƙarshen ɗigon ruwan har sai ya fita tsarkakke daga ƙananan zunubai idan ya gama alwalar.
Koyarwar hadisin: Idan bawa musulmi ya yi alwala - ko kuma mumini - sai y…
- Falalar kiyayewa akan alwala, kuma cewa ita tana kankare zunubai.
- Daga shiryarwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi yana kwaɗaitar da mutane a cikin ayyukan ɗa'a da kuma ibadu ta hanyar ambatan lada da sakamako akan su.
- Kowace gaɓa daga gaɓɓan mutum tana faɗawa cikin wani abu daga saɓo, saboda haka zunubai suke bin kowace gaɓar da ta aikatasu, kuma suna fita daga kowace gaɓar da ya tuba daga gareta.
- Alwala, a cikinta akwai tsarkaka ta gani ɓaro-ɓaro, kuma tana kasancewa ne a lokacin da kake wanke gaɓɓan alwala, da kuma tsarkakewa ta ma'ana tana kasancewa ne daga zunuban da suka faru daga gaɓɓan.
Rukunan :
FIƘHU NA IBADA
· TSARKI
· FALALOLI
· FALALOLIN AYYUKAN GAƁOƁI
· FIƘHU DA USULU
· ALWALA
· FALALOLI DA LADUBBA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
سبحان الله وبحمده
Tsarkin Allah da godiyarSa