Idan ɗayanku zai shiga masallaci, to, ya ce: Ya Allah Ka buɗe min ƙofofin rahamarKa, idan …
Musulunci > Ha > Hadith > Fihu na ibada > Idan ɗayanku zai shiga masallaci, to, ya ce: Ya Allah Ka buɗe min ƙofofin rahamarKa, idan …
Wanda ya ruwaito hadisin: Muslim ne ya rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Idan ɗayanku zai shiga masallaci, to, ya ce: Ya Allah K…
Bayanin hadisin: Idan ɗayanku zai shiga masallaci, to, ya ce: Ya Allah K…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya shiryar da al'ummarsa addu'ar da ake faɗa a yayin shiga masallaci: (Ya Allah ka buɗe min ƙofofin rahamarKa), sai ya roƙi Allah - Maɗaukakin sarki - Ya sawwaka masa hanyoyin rahamarSa, idan ya yi nufin fita, to, ya ce: (Ya Allah ina roƙonKa daga falalarKa), sai ya roƙi Allah daga falalarSa da ƙarin kyautatawarSa daga arziki na halal.
Koyarwar hadisin: Idan ɗayanku zai shiga masallaci, to, ya ce: Ya Allah K…
- An so wannan adddu'ar a yayin shiga masallaci da fita daga cikinsa.
- Keɓance ambaton rahama a shiga, da falala a fita: saboda mai shiga ya shagalta da abin da zai kusanto da shi zuwa ga Allah da kuma aljannarSa, sai ya dace da ya ambaci rahama, idan ya fita zai tafi a ban ƙasa don neman falalar Allah da arziki, sai ya dace da ambaton falala.
- Waɗannan zikiran ana faɗinsu ne yayin nufin shiga masallaci, da yayin nufin fita daga cikinsa.
Rukunan :
FIƘHU NA IBADA
· SALLAH
· FIƘHUN ADDU'O'I DA ZIKIRAI
· ZIKIRAI NA SHIGA DA FITA DAGA MASALLACI
· FIƘHU DA USULU
· FALALOLI DA LADUBBA
· HUKUNCE-HUKUNCEN MASALLATAI
بسم الله الرحمن الرحيم
Lar 16 Jumada al-Awwal
الأربعاء 16 جمادى الأولى
سبحان الله وبحمده
Tsarkin Allah da godiyarSa