Kara Ruku'u 539 na Alkur'ani

Ruku'u 539 daga Surah Al-Qadr ne (ayoyi 1 zuwa 5). Yana ɗauke da ayoyi 5 kuma yana cikin Juz 30.

An sabunta a 05 Agusta 2026 16h34

Ruku 539 a cikin Alkur'ani

5
ayoyi
1
Surah
30
Juz
v.1 – v.5
Ayoyi

Surori a cikin Ruku 539

القدر · Juz 30
Kewaya
Alamomi
Sauti
Hadda
Nuni
Shafi 598
◄ Ruku'u 539 ►
سورة القدر
Juz 30 80.3% (453/564)
Hizb 60 61.5% (177/288)

إِنَّآ أَنزَلْنَـٰهُ فِى لَيْلَةِ ٱلْقَدْرِ ﴿1﴾

Lalle ne Mũ, Mun saukar da shi (Alƙur'ãni) a cikin Lailatul ƙadari (daren daraja)

وَمَآ أَدْرَىٰكَ مَا لَيْلَةُ ٱلْقَدْرِ ﴿2﴾

To, me ya sanar da kai abin da ake cewa Lailatul ¡adari?

لَيْلَةُ ٱلْقَدْرِ خَيْرٌۭ مِّنْ أَلْفِ شَهْرٍۢ ﴿3﴾

Lailatul ¡adari mafi alheri ne daga wasu watanni dubu.

تَنَزَّلُ ٱلْمَلَـٰٓئِكَةُ وَٱلرُّوحُ فِيهَا بِإِذْنِ رَبِّهِم مِّن كُلِّ أَمْرٍۢ ﴿4﴾

Mala'iku da Rũhi suna sauka a cikinsa da iznin Ubangijinsu sabõda kowane umurni.

سَلَـٰمٌ هِىَ حَتَّىٰ مَطْلَعِ ٱلْفَجْرِ ﴿5﴾

Sallama ne shi daren, har fitar alfijiri.

بسم الله الرحمن الرحيم Jum 26 Rabi' al-Thani
الجمعة 26 ربيع الآخر
هلال متناقص Gajimaren Raguwa Rana 27.8 / 29.5
Haske 3%
Wata Sabo a cikin kwana 2
حسبنا الله ونعم الوكيل Allah Ya isa mana, Shi ne mafi kyawun Mai Kiyaye

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah