Ku saurara lallai cewa duniya tsinanniya ce, kuma abinda ke cikinta ma tsinanne ne, sai am…
Musulunci > Ha > Hadith > Abubuwa masu tausasa zukata da waazozi > Ku saurara lallai cewa duniya tsinanniya ce, kuma abinda ke cikinta ma tsinanne ne, sai am…
Wanda ya ruwaito hadisin: Tirmizi ne ya Rawaito shi
Hasan ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Ku saurara lallai cewa duniya tsinanniya ce, kuma abind…
Bayanin hadisin: Ku saurara lallai cewa duniya tsinanniya ce, kuma abind…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa duniya da abinda ke cikinta abin ƙine a wurin Allah abin zargi abin bari abin nisantarwa, kuma abinda ke cikinta abin bari ne ba abin yabo bane; dan kasancewarta da dukkan abinda ke cikinta yana shagaltarwa daga barin Allah, kuma yana nisantarwa daga gare shi, saidai ambatan Allah da abinda ya kusance shi ya zama yana da jinsi da shi, cikin abinda Allah Ya so shi, ko masanin ilimi na shari'a wanda yake koyar da mutane, ko mai neman ilimin shari'a ɗin.
Koyarwar hadisin: Ku saurara lallai cewa duniya tsinanniya ce, kuma abind…
- La'antar duniya ba ta halatta kai tsaye; dan zuwan hadisan da suke hani daga hakan, saidai la'antar abinda ke nisantarwa daga Allah - Maɗaukakin sarki - a cikinta kuma yake shagaltarwa daga biyayyrSa to yana halatta.
- Dukkan abinda ke cikin duniya to wasa ne kuma shagala ne sai ambatan Allah da abinda yake sababi kuma mai taimako a cikin hakan.
- Bayanin falalar ilimi da ma'abotansa da kuma ɗalibansa.
- Ibnu Taimiyya ya ce: Kaɗai ana zargin haramun ne bata fuskarsa ba, ko halal ta hanyar neman yawaitawa da alfahari, da abinda ake riƙa dan nufin fariya da gasa, to wannan shi ne wanda yake abin ƙi gurin masu hankali.
Rukunan :
ABUBUWA MASU TAUSASA ZUKATA DA WA'AZOZI
· ZARGIN SON DUNIYA
· FALALOLI DA LADUBBA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
الحمد لله
Alhamdulillah - Godiya ta tabbata ga Allah