Alkiyama ba zata tashi ba har sai rana ta bullo ta mafadarta, idan ta bullo mutane suka g…

Musulunci > Ha > Hadith > Alurani mai girma da ilimansa > Alkiyama ba zata tashi ba har sai rana ta bullo ta mafadarta, idan ta bullo mutane suka g…

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 1

Rubutun hadisin: Alkiyama ba zata tashi ba har sai rana ta bullo ta maf…

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ: أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «لاَ تَقُومُ السَّاعَةُ حَتَّى تَطْلُعَ الشَّمْسُ مِنْ مَغْرِبِهَا، فَإِذَا طَلَعَتْ فَرَآهَا النَّاسُ آمَنُوا أَجْمَعُونَ، فَذَلِكَ حِينَ: {لاَ يَنْفَعُ نَفْسًا إِيمَانُهَا لَمْ تَكُنْ آمَنَتْ مِنْ قَبْلُ، أَوْ كَسَبَتْ فِي إِيمَانِهَا خَيْرًا} [الأنعام: 158] وَلَتَقُومَنَّ السَّاعَةُ وَقَدْ نَشَرَ الرَّجُلاَنِ ثَوْبَهُمَا بَيْنَهُمَا فَلاَ يَتَبَايَعَانِهِ، وَلاَ يَطْوِيَانِهِ، وَلَتَقُومَنَّ السَّاعَةُ وَقَدِ انْصَرَفَ الرَّجُلُ بِلَبَنِ لِقْحَتِهِ فَلاَ يَطْعَمُهُ، وَلَتَقُومَنَّ السَّاعَةُ وَهُوَ يَلِيطُ حَوْضَهُ فَلاَ يَسْقِي فِيهِ، وَلَتَقُومَنَّ السَّاعَةُ وَقَدْ رَفَعَ أَحَدُكُمْ أُكْلَتَهُ إِلَى فِيهِ فَلاَ يَطْعَمُهَا».

Bayanin hadisin: Alkiyama ba zata tashi ba har sai rana ta bullo ta maf…

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa daga alamomin Alkiyama manya; shi ne bullowar rana daga yamma maimakon daga gabas, lokacin da mutane suka ganta za su yi imani gaba daya, A wannan lokacin imanin kafiri ba zai anfanar da shi ba, kuma aiki na gari ba zai yi amfani ba haka kuma tuba. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Alkiyama zata zo kwatsam; har cewa ita zata tashi alhali mutane suna cikin harkokin su da kuma sha'aninninkan rayuwarsu; Sai Alkiyama ta tashi alhali mai siyarwa da mai saya sun shimfida tufafinsu a tsakakninsu, amma ba za su saida su ba, ba kuma za su ninke su ba. Kuma Alkiyama zata tashi alhali hakika mutum ya dauki nonon taguwarsa mai yawan nono amma ba zai sha shi ba, Alkiyama za ta tashi alhali mutum yana gyara tafkinsa yana tsaftace shi amma ba zai shayar a cikinsa ba, Alkiyama za ta tashi alhali mutum ya daga lomarsa zuwa bakinsa dan ya ci amma ba zai ci ba.

Koyarwar hadisin: Alkiyama ba zata tashi ba har sai rana ta bullo ta maf…

Rukunan : ALƘUR'ANI MAI GIRMA DA ILIMANSA · TAFSIRIN ALƘUR'ANI · ILIMIN AƘIDA · Imani da Ranar Lahira · TAFSIRIN AYOYI · RAYUWAR BARZAHU

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
حسبنا الله ونعم الوكيل Allah Ya isa mana, Shi ne mafi kyawun Mai Kiyaye

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah