Lallai cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya zo w…

Musulunci > Ha > Hadith > Alurani mai girma da ilimansa > Lallai cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya zo w…

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari ne ya rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 1

Rubutun hadisin: Lallai cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata…

عَنْ ‌عَائِشَةَ رضي الله عنها: أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ إِذَا أَوَى إِلَى فِرَاشِهِ كُلَّ لَيْلَةٍ جَمَعَ كَفَّيْهِ، ثُمَّ نَفَثَ فِيهِمَا فَقَرَأَ فِيهِمَا: {قُلْ هُوَ اللهُ أَحَدٌ}، وَ{قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ الْفَلَقِ}، وَ{قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ النَّاسِ}، ثُمَّ يَمْسَحُ بِهِمَا مَا اسْتَطَاعَ مِنْ جَسَدِهِ، يَبْدَأُ بِهِمَا عَلَى رَأْسِهِ وَوَجْهِهِ وَمَا أَقْبَلَ مِنْ جَسَدِهِ، يَفْعَلُ ذَلِكَ ثَلَاثَ مَرَّاتٍ.

Bayanin hadisin: Lallai cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata…

Ya kasance daga shiriyarsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - idan ya zo wa shinfidarsa dan ya yi bacci yana tara tafikansa biyu sai ya daga su - kamar yadda mai addu'a yake yi - sai ya yi tofi a cikinsu daga bakinsa sassaukan tofi tare da yawu sassauka sai ya karanta surori uku: {Ka ce Shi ne Allah Shi kadai} da {Ka ce ina neman tsari da Ubangijin safiya} da {Ka ce ina neman tsari da Ubangijin mutane}, sannan ya shafi abinda zai yi wu daga jikinsa; yana mai farawa da kansa da fuskarsa da bangare na gaba daga jikinsa, yana maimaita wannan aikin sau uku.

Koyarwar hadisin: Lallai cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata…

Rukunan : ALƘUR'ANI MAI GIRMA DA ILIMANSA · FALALOLI NA ALƘUR'ANI · LADUBBA NA SHARI'A · LADUBBAN BARCI DA FARKAWA · FALALOLI NA SURORI DA AYOYI · FALALOLI DA LADUBBA

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
أستغفر الله Ina neman gafara daga Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah