Haƙiƙa an saukar mini da wata aya ita ce mafi soyuwa gareni daga duniya da abinda ke cik…

Musulunci > Ha > Hadith > Alurani mai girma da ilimansa > Haƙiƙa an saukar mini da wata aya ita ce mafi soyuwa gareni daga duniya da abinda ke cik…

Wanda ya ruwaito hadisin: Muslim ne ya rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Haƙiƙa an saukar mini da wata aya ita ce mafi soyuwa g…

Bayanin hadisin: Haƙiƙa an saukar mini da wata aya ita ce mafi soyuwa g…

Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa lokacin da faɗinSa - Allah Maɗaukakin sarki - ya sauka ga manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: {Haƙiƙa mu mun yi maka buɗi buɗi mabayyani (1).

Dan Allah Ya gafarta maka abinda ya gabata daga zunubinka da wanda ya jinkirta, kuma Ya cika ni'imarSa gareka kuma Ya shiryar da kai hanya madaidaiciya (2).

Kuma Ya taimake ka taimako mai girma (3).

Shi ne wanda Ya sanya nutsuwa a cikin zukatan muminai dan su ƙara imani tare da imaninsu, rundunonin sammai da ƙasa nasa ce, kuma Allah Ya kasance Masani Mai hikima (4).

Dan ya shigar da muminai maza da mata aljannatai ƙoramu suna gudana ta ƙarƙashinsu suna masu dawwama a cikinsu kuma Ya kankare musu munananan ayyukansu hakan ya kasance rabo mai girma a wurin Allah} [al-Fath: 1-5].

A lokacin dawowarsa daga Hudaibiyya, su kuma sahabbai bakin ciki da bacin rai ya turnuke su, kuma an hana su yin Umarah, saboda abinda sulhun ya faru a kansa da kuma zatansu cewa sulhun ba’a yi shi akan maslahar musulmai ba, hakika kuma sun yanka hadaya a Hudaibiyya, sai (annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Haƙiƙa an saukar mini da wata aya wacce ita ce mafi soyuwa gareni daga duniya bakiɗayanta sannan ya karantata.

Koyarwar hadisin: Haƙiƙa an saukar mini da wata aya ita ce mafi soyuwa g…

Rukunan : ALƘUR'ANI MAI GIRMA DA ILIMANSA · TAFSIRIN ALƘUR'ANI · FALALOLI NA ALƘUR'ANI

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 97%
Wata Sabo a cikin kwana 13
سبحان الله Subhanallah - Tsarkin Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah