Allah ba ya karbar sallar dayanku idan ya yi hadasi har sai ya yi alwala
Musulunci > Ha > Hadith > Fihu na ibada > Allah ba ya karbar sallar dayanku idan ya yi hadasi har sai ya yi alwala
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Allah ba ya karbar sallar dayanku idan ya yi hadasi har…
Bayanin hadisin: Allah ba ya karbar sallar dayanku idan ya yi hadasi har…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa daga sharuddan ingancin sallah: Tsarki, to yana wajaba akan wanda ya yi nufin sallah ya yi alwala, in ya kasance wani abu mai warware alwala daga masu warware alwala ya faru agare shi; kamar bayan gida ko fitsari ko bacci ko wasunsu.
Koyarwar hadisin: Allah ba ya karbar sallar dayanku idan ya yi hadasi har…
- Sallar wanda ba shi da tsarki ba'a karbarta har sai ya yi tsarki, da yin wanka daga babban kari da kuma alwala daga karamin kari.
- Alwala ita ce daukar ruwa da motsashi a baki da kuma fitar da shi, sannan jawo ruwa da numfashinsa zuwa cikin hancinsa, sannan fitar da shi da face shi, sannan wanke fuskarsa sau uku, sannan wanke hannayensa tare da gwiwoyin hannu sau uku, sannan shafar dukkanin kansa sau daya, sannan wanke kafafuwansa tare da idon sawu sau uku.
Rukunan :
FIƘHU NA IBADA
· TSARKI
· FIƘHU DA USULU
· ALWALA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
لا حول ولا قوة إلا بالله
Babu wata ƙarfi ko iko sai na Allah