Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya koya mana jawabin fara maga…

Musulunci > Ha > Hadith > Fihu da usulu > Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya koya mana jawabin fara maga…

Wanda ya ruwaito hadisin: Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i da Ibn Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare…

عن عبد الله بن مسعود رضي الله عنه قال: عَلَّمَنَا رَسُوْلُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ خُطْبَةَ الحَاجَةِ: إِنَّ الحَمْدَ للهِ، نَسْتَعِيْنُهُ وَنَسْتَغْفِرُهُ، وَنَعُوْذُ بِهِ مِنْ شُرُوْرِ أَنْفُسِنَا، مَنْ يَهْدِ اللهُ فَلَا مُضِلَّ لَهُ، وَمَنْ يُضْلِلْ فَلَا هَادِيَ لَهُ، وَأَشْهَدُ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا الله، وَأَشْهَدُ أَنَّ مُحَمَّدًا عَبْدُهُ وَرَسُوْلُهُ، {يَا أَيُّهَا النَّاسُ اتَّقُوا رَبَّكُمُ الَّذِي خَلَقَكُمْ مِنْ نَفْسٍ وَاحِدَةٍ وَخَلَقَ مِنْهَا زَوْجَهَا وَبَثَّ مِنْهُمَا رِجَالًا كَثِيرًا وَنِسَاءً وَاتَّقُوا اللَّهَ الَّذِي تَسَاءَلُونَ بِهِ والأرحام إن الله كان عليكم رقيبا} [النساء: 1]، {يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اتَّقُوا اللَّهَ حَقَّ تُقَاتِهِ وَلَا تَمُوتُنَّ إِلَّا وَأَنْتُمْ مُسْلِمُونَ} [آل عمران: 102]، {يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اتَّقُوا اللَّهَ وَقُولُوا قَوْلًا سَدِيدًا (70) يُصْلِحْ لَكُمْ أَعْمَالَكُمْ وَيَغْفِرْ لَكُمْ ذُنُوبَكُمْ وَمَنْ يُطِعِ اللَّهَ وَرَسُولَهُ فَقَدْ فَازَ فَوْزًا عَظِيمًا} [الأحزاب:70 - 71].

Bayanin hadisin: Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare…

Dan Mas’ud Allah Ya yarda da shi, yana ba da labarin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya koya musu huɗubar buƙata, wato wadda ake faɗa lokacin buɗe magana a huɗubobi, da kuma kafin faɗin buƙatar mai jawabi, kamar huɗubar aure da huɗubar Juma’a da sauransu. Wannan huɗubar ta ƙunshi ma’anoni masu girman gaske na bayanin cacncantar Allah ga dukkanin nau’o'in yabo, da neman taimakonSa Shi kaɗai ba shi da abokin tarayya, da neman yafiyar zunubai da kankarewsu , da neman kariyarSa daga dukkan sharri, da sharrin kai da sauransu.

Sannan Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya ba da bayanin, ita shiriya tana hannun Allah ne, wanda kuma Ya shiryar da shi, to, babu mai ɓatar da shi, wanda kuma ya ɓatar, to, babu mai shiryar da shi.

Sannan ya ambaci shaidawa da Tauhidi, kuma babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, da shaidawa da Manzanci da cewa Annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) bawanSa ne kuma manzanSa ne.

Sai Kuma ya rufe wannan huɗubar da ayoyi guda uku waɗanda suka ƙunshi umarni da jin tsoron Allah maɗaukaki ta hanyar aikata umarninSa da kuma nisantar abin da Ya hana don neman yardar Allah, kuma sakamakon wanda ya aikata haka kyautatuwan ayyuka da maganganu da kankarewar zunubi da gafarta laifuka, da kuma kyakyawar rayuwa a duniya, da rabauta da aljanna ranar Alƙiyama.

Koyarwar hadisin: Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare…

Rukunan : FIƘHU NA ZAMANTAKEWAR IYALI · AURE · FIƘHU DA USULU · HUKUNCE-HUKUNCE DA SHARUƊAN AURE

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.6 / 29.5
Haske 96%
Wata Sabo a cikin kwana 13
اللهم صل على محمد Ya Allah, ka saukar da tsira a kan Muhammad

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah