Allah Ya ce: Ya kai Ɗan Adam, ka ciyar zan ciyar da kai
Musulunci > Ha > Hadith > Fihu da usulu > Allah Ya ce: Ya kai Ɗan Adam, ka ciyar zan ciyar da kai
Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Allah Ya ce: Ya kai Ɗan Adam, ka ciyar zan ciyar da kai
عن أبي هريرة رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «قَالَ اللهُ: أَنْفِقْ يَا ابْنَ آدَمَ أُنْفِقْ عَلَيْكَ».
Bayanin hadisin: Allah Ya ce: Ya kai Ɗan Adam, ka ciyar zan ciyar da kai
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana ba da labarin Allah maɗaukakin sarki Ya ce: Ya kai Ɗan Adam ka ciyar cikin ciyarwar wajibi da ta Mustahabbi zan yalwata maka, zan kuma ba ka makwafin abin da ka bayar, kuma in sanya maka albarka.
Koyarwar hadisin: Allah Ya ce: Ya kai Ɗan Adam, ka ciyar zan ciyar da kai
- Kwaɗaitarwa a kan sadaka da kuma ciyarwa Fi-sabilillahi.
- Ciyarwa ta ɓangarorin alheri yana daga cikin manyan dalilan samun albarka a arziki da kuma ninka shi, da kuma yadda Allah zai mayarwa bawa abin da ya ciyar.
- Wannan hadisin yana daga abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yake ruwaitoshi daga Ubangijinsa, ana ambatonsa da Hadisi Ƙudsi, ko Ilahi, shi ne wanda lafazinsa da ma'anarsa daga Allah ne, sai dai cewa shi babu keɓance-keɓancen Alkur’ani a cikinsa waɗanda ya keɓanta da su daga waninsa, kamar bauta da karantashi, da yin tsarki sabo da shi da fito na fito(ƙalubalanta) da gajiyarwa, da sauransu.
Rukunan :
FIƘHU NA IBADA
· FIƘHU NA ZAMANTAKEWAR IYALI
· ZAKKA
· CIYARWA
· FIƘHU DA USULU
· SADAKA TA NAFILA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
لا حول ولا قوة إلا بالله
Babu wata ƙarfi ko iko sai na Allah