Musulunci > Ha > Hadith > Fihu na ibada > Idan mutum ya rasu akin sa ya yanke sai dai daga abu uku: Sadaka mai gudana, ko wani ilimi…
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa aikin mamaci yana yankewa da rasuwarsa,, kyawawan ayyuka basa samunsa bayan mutuwnrsa sai a waɗannan ukun; dan kasancewarsa ya zama sababinsu:
Na farko: Sadakar da ladanta yake gudana kuma yake dawwama, ba mai yankewa ba, kamar waƙafi, da gina masallatai, da haƙa rijiyoyi, da wanin hakan.
Na biyu: Ilimin da mutane suke anfanuwa da shi, kamar wallafa littattafan ilimi, ko kamar ya koyar da wani mutum, sai wannan mutumin ya yaɗa wannan ilimin bayan mutuwarsa.
Na uku: Ɗa na gari mumini da zai yi masa addu'a.
Rukunan : FIƘHU NA IBADA · FIƘHU NA MU'AMALAT · JANA'IZA · WAƘAFI · FALALOLI · FALALAR ILIMI · FALALAR ADDU'A · FIƘHU DA USULU · Doing Good Deeds on behalf of the Deceased and Gifting them the Reward · FALALOLI DA LADUBBA · Merit and Significance of Knowledge