Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarce mu da abubuwa guda …

Musulunci > Ha > Hadith > Fihu na ibada > Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarce mu da abubuwa guda …

Wanda ya ruwaito hadisin: Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare…

Bayanin hadisin: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare…

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarci musulmai da ɗabi'u bakwai kuma ya hanesu ɗabi'u bakwai; waɗanda ya umarce su sune: Na farkonsu: Ziyarar mara lafiya. Na biyunsu: Raka jana'iza da tarayya ta hanyar yi mata sallah da kuma binneta, da yi mata addu'a. Na ukunsu: Yin addu'a ga wanda ya yi atishawa kuma ya godewa Allah, shi ne ace masa: Allah Ya yi maka rahama. Na huɗunsu: Kuɓutar da mai rantsuwa da kuma gasgata shi, ma'ana cewa da zai yi rantsuwa akan wani al'amari alhali kai kana da iko akan sanya shi kuɓutacce a cikinta to ka aikata; dan kada ka bar shi zuwa yin kaffara ta rantsuwar. Na biyarɗinsu: Taimakon wanda aka zalinta, ta hanyar taimaka masa da tunkuɗe abinda yake afka masa daga azzalimi gwargwadan iko. Na shidansu: Amsa gayyata zuwa walimar abin ci, kamar walimar angwanci, ko suna, ko waninsu. Na bakwansu: Yin sallama da yaɗata da kuma amsata. Waɗanda kuma ya hanasu su ne: Na farkonsu: Sanya zobunan zinare da kuma yin ado da su. Na biyunsu: Shan abu a ƙwaryar azirfa. Na ukunsu: Zama akan Mayasir, sune shimfiɗun da ake sawa akan sirdin doki da kuma sirdin raƙumi na alharaini. Na huɗunsu: Sanya tufafin da aka yi da kattanin da aka cakuɗa da alharini kuma ana ambatansa: (Alƙisiyyu). Na biyarɗinsu: Sanya alharaini. Na shidansu: Sanya Istabraƙ, shi ne: Alharini mai kauri. Na bakwansu: Sanya Dibaj, shi ne: Mafi kyan nau'ikan alharini kuma mafi tsadarsu.

Koyarwar hadisin: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare…

Rukunan : FIƘHU NA IBADA · JANA'IZA · LADUBBA NA SHARI'A · FIƘHU DA USULU · ƊAUKAR MAMACI DA BINNESHI · FALALOLI DA LADUBBA

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 97%
Wata Sabo a cikin kwana 13
أستغفر الله Ina neman gafara daga Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah