Musulunci > Ha > Hadith > Falaloli > Shin ba na nuna muku abin da Allah Ya ke shafe kurakurai da shi ba, kuma Yake ɗaukaka dara…
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 2Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya tambayi sahabbansa shin suna son ya nuna musu wasu ayyukan da za su zama sababi a gafarta zunubai, da shafesu daga littatttafan (mala'iku) masu kiyayewa, da ɗaukakar darajoji a cikin aljanna?
Sahabbai suka ce: Eh, muna son hakan. Ya ce:
Na farko: Gamewa da cika alwala a wahala; kamar (lokacin) sanyi da ƙarancin ruwa, da raɗaɗin jiki, da ruwan zafi.
Na biyu: Yawan takawa - shi ne abinda ke tsakanin diga-digai biyu - zuwa masallatai, ta nisan gida da Masallacin, da yawan maimaita zuwa Masallaci.
Na uku: Jiran lokacin sallah, da ratayar zuciya ga sallar, da yin tanadi gareta, da zama gareta a cikin masallatai dan jiran jama'a, idan ya sallace ta to ya jira wata sallar ta gaba a nan inda ya yi sallah.
Sannan tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi ya bayyana cewa waɗannan al'amuran su ne zaman dako na haƙiƙa; domin suna toshe hanyoyin Shaiɗan ga mutum, kuma suna rinjayar da son rai, kuma suna hana rai daga shiga waswasi, sai rundunar Allah su rinjayi rundunar Shaiɗan da su; Hakan shi ne jihadi mafi girma, sai suka zama a matsayin zaman dako a kafofin maƙiya.
Rukunan : FALALOLI · FALALOLIN AYYUKA NAGARI · FALALOLI DA LADUBBA