Musulunci > Ha > Hadith > Falaloli > Shin ba na baku labari da mafificin ayyukanku ba, kuma mafi tsarkinsu a gurin Mamallakinku…
Ingantacce neAn sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tambayi sahabbansa:
Shin kuna son in baku labari ? In sanar da ku da mafificin ayyukanku, kuma mafi ɗaukakarsu, mafi ƙaruwarsu, mafi tsarkinsu, mafi tsaf-tsaf ɗinsu a wurin Allah Mamallaki - Mai girma da ɗaukaka -?
kuma mafi ɗaukakarsu a cikin masaukanku a aljanna?
kuma mafi alheri gareku daga sadaka da zinare da azirfa?
Kuma mafi alheri a gareku daga ku haɗu da kafirai dan yaƙi, sai ku daki wuyansu, su daki wuyanku ?
Sahabbai suka ce: Eh, muna son hakan.
(Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Ambatan Allah - Maɗaukakin sarki - a dukkan lokuta da kuma dukkan siffofi da halaye.
Rukunan : FALALOLI · FALALOLIN ZIKIRI · FALALOLI DA LADUBBA