Shin ba na nuna muku abin da Allah Ya ke shafe kurakurai da shi ba, kuma Yake ɗaukaka dara…

Musulunci > Ha > Hadith > Falaloli > Shin ba na nuna muku abin da Allah Ya ke shafe kurakurai da shi ba, kuma Yake ɗaukaka dara…

Wanda ya ruwaito hadisin: Muslim ne ya rawaito shi

Ingantacce ne

An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26

📖 Karatu minti 2

Rubutun hadisin: Shin ba na nuna muku abin da Allah Ya ke shafe kurakura…

Bayanin hadisin: Shin ba na nuna muku abin da Allah Ya ke shafe kurakura…

Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya tambayi sahabbansa shin suna son ya nuna musu wasu ayyukan da za su zama sababi a gafarta zunubai, da shafesu daga littatttafan (mala'iku) masu kiyayewa, da ɗaukakar darajoji a cikin aljanna?

Sahabbai suka ce: Eh, muna son hakan. Ya ce:

Na farko: Gamewa da cika alwala a wahala; kamar (lokacin) sanyi da ƙarancin ruwa, da raɗaɗin jiki, da ruwan zafi.

Na biyu: Yawan takawa - shi ne abinda ke tsakanin diga-digai biyu - zuwa masallatai, ta nisan gida da Masallacin, da yawan maimaita zuwa Masallaci.

Na uku: Jiran lokacin sallah, da ratayar zuciya ga sallar, da yin tanadi gareta, da zama gareta a cikin masallatai dan jiran jama'a, idan ya sallace ta to ya jira wata sallar ta gaba a nan inda ya yi sallah.

Sannan tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi ya bayyana cewa waɗannan al'amuran su ne zaman dako na haƙiƙa; domin suna toshe hanyoyin Shaiɗan ga mutum, kuma suna rinjayar da son rai, kuma suna hana rai daga shiga waswasi, sai rundunar Allah su rinjayi rundunar Shaiɗan da su; Hakan shi ne jihadi mafi girma, sai suka zama a matsayin zaman dako a kafofin maƙiya.

Koyarwar hadisin: Shin ba na nuna muku abin da Allah Ya ke shafe kurakura…

Rukunan : FALALOLI · FALALOLIN AYYUKA NAGARI · FALALOLI DA LADUBBA

بسم الله الرحمن الرحيم Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
بدر Cikakken Wata Rana 16.5 / 29.5
Haske 97%
Wata Sabo a cikin kwana 13
لا إله إلا الله Babu abin bautawa sai Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah