Lokacin da aka hau da ni (aka yi Mi'iraji da ni) na wuce wasu mutane da suke da farata na …
Musulunci > Ha > Hadith > Abubuwa masu tausasa zukata da waazozi > Lokacin da aka hau da ni (aka yi Mi'iraji da ni) na wuce wasu mutane da suke da farata na …
Wanda ya ruwaito hadisin: Abu Dawud ne Ya Rawaito shi
Hasan ne
An sabunta a 26 Oktoba 2026 23h26
📖 Karatu minti 1
Rubutun hadisin: Lokacin da aka hau da ni (aka yi Mi'iraji da ni) na wuc…
Bayanin hadisin: Lokacin da aka hau da ni (aka yi Mi'iraji da ni) na wuc…
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa shi: Lokacin da aka hau da shi zuwa sama a daren Isra'i da Mi'iraji, ya wuce wasu mutane suna da farata na tagulla suna yakusa suna yayyaga fuskokinsu da ƙirazansu da su, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya tambayi (Mala’ika) Jibril - aminci ya tabbata agare shi -: Me waɗannan mutanen suka aikata har ake musu sakayya da wannan azabar? Sai (Mala’ika) Jibril - aminci ya tabbata agare shi - ya ce: Waɗanan sune waɗanda suke yi da mutane, kuma suke magana a kan mutuncinsu ba tare da gaskiya ba.
Koyarwar hadisin: Lokacin da aka hau da ni (aka yi Mi'iraji da ni) na wuc…
- Gargaɗarwa mai tsanani daga yi da mutum, da kuma kamanta mai yi da mutum da wanda yake cin naman 'dan Adam.
- Afkawa cikin mutuncin mutane yana daga yi da mutum da makamancinsa na manyan zunubai.
- Al-Ɗaibi ya faɗa a cikin faɗinsa: "Suna yakusa", ya ce: Yayin da yakusar fuska da ƙirji suka zama daga cikin siffofin mata masu kukan mutuwa sai aka sanya hakan sakayyar wanda yake yi da mutane, kuma yake cin mutuncin musulmai, dan sanarwa da cewa su ba sa daga cikin siffofin maza, kai su suna daga cikin siffofin mata a cikin mafi munin hali kuma mafi munin sura.
- Wajabcin yin imani da gaibu da kuma dukkanin abinda Allah da ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - suka bada labari da shi.
Rukunan :
ABUBUWA MASU TAUSASA ZUKATA DA WA'AZOZI
· ZARGIN AYYUKAN SAƁO
· FALALOLI DA LADUBBA
بسم الله الرحمن الرحيم
Tal 15 Jumada al-Awwal
الثلاثاء 15 جمادى الأولى
سبحان الله
Subhanallah - Tsarkin Allah